logo

HAUSA

Matasa dubu 7 za su gudanar da aikin sa kai na tabbatar da tsaro a jihar Kaduna

2023-10-18 09:11:50 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya ta bi sahun sauran jihohin dake shiyyar da suke fama da matsalolin tsaro wajen samar da rundunar sa kai ta musamman da za su yi aiki da sauran jami’an tsaro wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda a jihar.

Tun dai a farkon watan jiya na Satumba ne matasan suka fara samun horo a kwalejin horas da ’yan sanda dake garin Kaduna, wanda kuma suka kammala samun horo a wannan mako.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Daman dai da jimawa gwamnatin jihar Kaduna ta samar da runduna ta tsaro mai suna KADVS da take taimakawa jami’an tsaron jihar, a jawabinsa na bikin cika kwanaki 100 gwamnan jihar Sanata Ubah Sani ya yi alkawarin kara yawan dakarun rundunar domin kara karfin aikinta yadda ya kamata.

Su dai wadannan matasa da suka kunshi maza da mata an zabo su ne daga kananan hukumomin jihar 23, kuma sun samu cikakken horo da ya kamata da za su hadu da sauran jami’an tsaro wajen fatattakar ’yan ta’adda daga mafakar da suke a boye.

Yayin tsawon lokacin da aka dauka ana baiwa matasan horon, an ja hankalinsu a kan kiyaye hakkin dan Adam yayin da suke gudanar da aiki, kamar dai daya daga cikin jami’an bayar da horon ya shaidawa manema labarai.

“Ko da wani abu ne mutum ya yi musu tabbatar da cewa, sun bi doka yadda ya kamata, amma ba wai daukar doka a hannu ba, wasun su mafarauta ne a baya idan sun kama mutum suna karya shi ne nan take kafin su kai shi wajen jami’an tsaro, amma mun gaya masu ba a yi haka, su tabbatar da cewa sun mutunta hakkin mutane, kuma mun karanta masu yadda ya kamata, kuma mun tabbatar da cewa sun fahimci abin da ake nufi.”

Ko me matasan da aka dauka za su ce game da wannan aiki?

“Gaskiya na ji dadi sosai domin da ma ina cikin wannan harka ta tsaro. Da wata kungiya muke yi sa kai domin mu ne muka fitini barayin yankin Soba har ma da na wasu yankunan, sai kuma ga shi gwamna ya taimaka ya ba mu wannan aiki, abun dai da muke fata shi ne Allah ya sa ya samar mana da kayan aiki isasshe.”

“Abun da ya janyo hankalina na shiga wannan aiki shi ne domin na taimakawa al’umma da kasa ta, mun samu horo mun kuma gama cikin koshin lafiya, muna godiya ga Allah, kuma alkawari da muka dauka shi ne za mu yi aiki cikin gaskiya cikin aminci in Allah ya yarda, ba za mu ba shi kunya ba.” (Garba Abdullahi Bagwai)