logo

HAUSA

Sakatare Janar MDD ya ce ya firgita da harin asibitin Gaza

2023-10-18 10:35:21 CMG Hausa

A jiya Talata ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani asibiti a gaza. Yana mai cewa ya kadu da kisan daruruwan Falasdinawa fararen hula. 

A kalla Falasdinawa 500 aka kashe a wannan kazamin harin da aka kai kan asibitin Al Ahli Arab da ke birnin Gaza.

Hamas dai ta zargi Isra’ila da kai harin, yayin da Isra’ila ta ce harin makamin roka ne da ya gaza da kungiyar Jihadi ta Falasdinu ta harba, wanda ita ma kungiyar ta musanta hannu a harin. 

Adadin wadanda suka mutu a Gaza ya kai 3,000 a wannan mummunar yakin da yanzu ya kai kwanaki 11 ana gwabzawa, a cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu. Yayin da adadin wadanda suka mutu a Isra’ila ya kai 1,300, wanda akasarinsu a ranar 7 ga Oktoban nan a harin ba-zata da Hamas ta kai kan al’ummonin kudancin kasar aka kashe su. (Muhammed Yahaya)