logo

HAUSA

Tabbatar da daidaito da cin moriyar juna suna cikin babban ruhin shawarar BRI

2023-10-18 20:58:23 CMG Hausa

Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI), wata shawara ce ta hadin gwiwar kasa da kasa, da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2013. Zuwa yanzu, kasar ta riga ta kulla takardun hadin gwiwa tare da kasashe fiye da 150, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30, da gudanar da ayyukan hadin gwiwa fiye da 3000, da janyo jarin da ya kai dalar Amurka fiye da triliyan 1, duk a karkashin shawarar BRI.

A yau, an yi bikin kaddamarwar taron koli na hadin gwiwar kasa da kasa a karkashin shawarar BRI karo na 3, a birnin Beijing na kasar Sin, wanda ya samu halartar manyan kusoshin kasashen fiye da 140, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30, ciki har da mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Kashim Shettima.

A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bikin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, shawarar BRI ta fi dora muhimmanci kan hadin gwiwa da taimakawa juna, inda ake neman tabbatar da cin moriya da ci gaba tare.

Game da tunanin cin moriya, tare da samun ci gaba tare da shawarar BRI ta kunsa, wasu abokai su kan nuna shakku, inda sukan ce, “ Ku Sinawa kuna zuwa Najeriya ne ba domin moriyar kanku ba?” Sai dai a hakika, alfanun shawarar BRI ya riga ya fito fili sosai a Najeriya.

Misali, a jihar Lagos, akwai wani kamfanin sarrafa kayan kwalliya na shafe-shafe, wanda ke bukatar shigar da wasu sinadarai daga ketare. Sai dai ma’aikatan kamfanin sun fi damuwa, lokacin da sinadaran da suke bukata suka iso tashar jirgin ruwa ta Apapa. Ina dalili? Saboda a kan samu cunkuso a tashar Apapa, inda dimbin motocin daukar kaya ke jiran a kwashe kayayyaki daga jiragen ruwa. Ko da yake ba nisa tsakanin tasha da kamfanin, amma a kan dauki wata daya kafin a iya kai kaya zuwa kamfanin. Sai dai yanayin ya sauya, bayan da aka fara yin amfani da babbar tashar jiragen ruwa ta Lekki, wadda aka gina ta karkashin shawarar BRI. Yanzu bayan da kayan kamfanin ya iso tashar, cikin kwanaki 7 za a iya samun kayan. Ta haka, kamfanin ya samu tsimin kudin da yake kashewa, saboda ba bukatar biyan karin kudi, idan an iya fitar da kaya daga cikin tasha cikin kwanaki 14.

Akwai dimbin kamfanonin da suka yi kama da wannan kamfanin da muka ambata, wadanda suka samu muhallin gudanar da ciniki mai inganci sakamakon kafuwar tashar ruwa ta Lekki. Yanzu haka sun samu kwarin gwiwar zuba karin jari a Najeriya, da daukar karin ma’aikata. Hakan shi ma ya sa yankin ciniki mai ‘yanci na Lekki, da kasashen Najeriya da Sin suka kafa cikin hadin kai bisa shawarar BRI, samun ci gaba sosai. Zuwa watan Yunin bana, akwai kamfanoni 175 da suka yi rajista a yankin, ciki har da kamfanonin Sin 73, da kamfanonin kasa da kasa 43. Kana a farkon watannin 6 na bana, kamfanonin da ke cikin yankin sun shigar da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 28, da fitar da kayan na dala miliyan 70 zuwa ketare. Ta wannan yanayi na sa kaimi ga masana’antu da ciniki, ana sa ran ganin tashar Lekki ta samar da kudin shiga har dala biliyan 361, da guraben aikin yi dubu 170 ga kasar Najeriya, cikin shekaru 45 masu zuwa.

Daga misalin tashar jirgin ruwa ta Lekki, za mu iya ganin yadda ake gudanar da hadin gwiwa a karkashin shawarar BRI: Da farko ana gina kayayyakin more rayuwa don tabbatar da hadewar yankuna daban daban, sa’an nan za a samu kyautatuwar muhallin kasuwanci, da sa kaimi ga ciniki da zuba jari, ta yadda za a tabbatar da ci gaban tattalin arzikin daukacin yankin da ake ciki. Ta wannan hanya, Sinawa za su iya samun riba bisa jarin da suka zuba, yayin da mutanen Najeriya su ma za su samu biyan bukatarsu, ta raya kasa, da kyautata zaman rayuwa.

Sai dai, a ko ina, ba za a rasa mutane masu nuna shakku ba. Kamar yadda wasu kan ce, “Shawarar BRI na da kyau, amma tana sanya kasashen Afirka cikin tarkon bashi”. Sai dai idan an kara yin bincike kan maganar, za a gane cewa ba ta da tushe ko kadan. Idan shawarar BRI na da wannan mummunar illa, anya za a ci gaba da samun kasashe fiye da 150 da suke son shiga cikin ta?

A hakika, alkaluman bankin duniya sun nuna cewa, masu jari na kasashen yamma sun fi bin kasashen Afirka bashi, yayin da bashin da kasar Sin ta bayar bai wuce kashi 17% kacal ba, cikin dukkan basussukan da kasashen Afirka suka ci. Ban da haka, kasar Sin ta dade tana samar da rancen kudi dake bukatar biyan ruwa kadan, ga kasashe marasa karfi dake nahiyar Afirka, gami da kokarin shiga shawarar daina biyan bashi ta kungiyar G20, inda ta kulla yarjejeniyar daina biyan bashi, ko kuma cimma matsaya a wannan fanni, tare da kasashe 19 dake nahiyar Afirka. Kana wani abun da ya fi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta dade tana kokarin tattaunawa tare da sauran kasashe, kan yadda za su iya yin hadin gwiwa bisa matsayi na daidai wa daida. Saboda haka, rancen da kasar Sin ta samar, ba zai yi kama da rancen kasashen yamma ba, wanda ya zama abin da suke yin amfani da shi wajen shawo kan kasashen Afirka.

Su kasashen yamma su kan nuna girman kai, yayin da suke hulda da kasashe masu tasowa, inda suke ikirarin cewa “Gaskiya tana hannuna.” Wannan tunani an gaje shi ne daga lokacin mulkin mallaka. A nata bangare, kasar Sin ba ta da wannan tunani na ‘yan mulkin mallaka. Saboda ta kasance daya daga cikin kasashe masu tasowa, inda take koyon fasahohin kasashen yamma, da lalubo turbar raya kasa ta kai, sa’an nan sannu a hankali, ta kai matsayi na yanzu. Saboda haka kasar Sin tana iya zama cikin daidaito tare da sauran kasashe masu tasowa, da son tattaunawa tare da su, don neman hanyar da za a bi, a kokarin tabbatar da ingancin hadin gwiwar da ake yi karkashin shawarar BRI. Wannan ne ma ya sa shugaba Xi Jinping, ya mai da kyautata tsarin hadin gwiwa karkashin shawarar BRI wani aiki mai muhimmanci, cikin jawabin da ya bayar a yau. Wato a tattauna kafin a aiwatar da wani mataki, da yin gyara a kai a kai, don mai da shawarar BRI wani abun da zai tabbatar da cin moriya tare da samun ci gaba tare, kuma ta haka ne ake tabbatar da kyakkyawar makoma ga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. (Bello Wang)