logo

HAUSA

Yadda Shawarar BRI Ta Zama Shiri Mafi Samun Karbuwa A Duniya Cikin Shekaru Goma Da Suka Gabata

2023-10-18 08:02:47 CMG Hausa

A wannan makon ne ake gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na uku ko BRF a takaice, da ya hada kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, da kuma bikin cika shekaru 10 da gabatar da shawarar “Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya” ko BRI. Taron wata muhimmiyar hanya ce ga masu tsara manufofi, abokan raya kasa da kasa, da sauran masu ruwa da tsaki, don yin musayar kwarewa, da bude sabbin damammaki na samun bunkasuwa a karkashin kokarin da kasar Sin ke jagoranta na tinkarar kalubalen duniya.

Hankalin kasashen duniya ya karkata zuwa ga wannan taro duba ga irin alfanu da fa’idojin dake tattare da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Yayin da kasashe masu tasowa ke kallon BRI a matsayin tushen samar da kudade, zuba jari, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa wanda zai iya bunkasa ci gaban tattalin arzikinsu da ci gabansu. Kaza lika, wasu kasashen suna kallon BRI a matsayin wata hanya ta daidaita shingaye dake kawo cikas ga ci gaban kasashe masu tasowa da wasu yankunan kamar Amurka ko Japan suka kafa. BRI na samar da wasu hanyoyin samar da tsaro, kwanciyar hankali, da dogaro ga wadannan kasashe, musamman a yankunan da suke fuskantar takaddamar tsakanin juna, da gabar siyasa, ko matsin lamba daga waje.  

Ana tsammanin samun sakamako mai kyau a wannan dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku ta hanyar tsara sabon jadawali ko takardar aikin kungiyar, tare da gudanar da manyan taruka guda uku kan hadin gwiwa, da ci gaban koren muhalli, da tattalin arzikin fasahar zamani na dijital, a bisa jigo shida da suka shafi hada-hadar kasuwanci, dangantakar jama’a da jama’a, musayar ra’ayi, hanyar siliki mai tsafta, hadin gwiwar kasa da kasa, da hadin gwiwar harkokin teku. (Muhammed Yahaya, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)