logo

HAUSA

Putin ya ce shawarar “ziri daya da hanya daya” na da muhimmanci, da nasaba da duniya, kuma tana la’akari da gaba

2023-10-18 16:43:01 CMG Hausa

A yau Laraba ne shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, shirin shawara “ziri daya da hanya daya” wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar yana da muhimmanci, kuma yana da nasaba da duniya da kuma gaba.

Mr. Putin ya bayyana hakan ne a wajen bikin bude taron tattaunawar hadin gwiwa na kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya karo na uku.

Yayin da yake yabawa shirin, Putin ya ce, Rasha da Sin suna da burin samun ci gaba mai dorewa a duniya, da kyautata zaman rayuwar jama'a, tare da mutunta bambancin wayewar kai, da 'yancin kowace kasa ta rungumi hanyar ci gabanta.

A kan wadannan ka’idoji na asali ne aka gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, a cewar Putin. (Muhammed Yahaya)