logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a tsagaita bude wuta tsakanin Falasdinu da Isra'ila

2023-10-17 19:05:13 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, Zhang Jun, ya yi kira da a tsagaita bude wuta tsakanin kasar Isra'ila da bangaren Falasdinawa, don kare fararen hula. Zhang ya yi kiran ne yayin taron kwamitin sulhun MDD da ya gudana a jiya Litinin.

Ya ce fada ya barke tun a kwanan baya tsakanin sassan biyu, wanda kuma ya yi sanadin rasa rayukan dimbin fararen hula, da haifar da matsala a fannin ayyukan jin kai, tare da haifar da mummunan tasiri ga yanayin tsaron daukacin yankin baki daya, lamarin da ya sa kasar Sin nuna damuwa sosai.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da duk wani mataki na lahanta fararen hula, da adawa da duk wani aiki na sabawa dokokin kasa da kasa. (Bello Wang)