logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya gaza cimma matsaya kan Gaza

2023-10-17 14:20:36 CMG Hausa

A jiya ne, kwamitin sulhun MDD ya gaza amincewa da wani kuduri da kasar Rasha ta zartas, wanda ya bukaci a tsagaita bude wuta a Gaza.

Daftarin kudurin ya samu kuri’un amincewa guda biyar, yayin da hudu suka ki amincewa, sai kuma guda 6 suka ki kada kuri’unsu.

Kasashe hudu sun bi sahun kasar Rasha wajen kada kuri’ar amincewa da kudurin, wato kasashen Sin, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Mozambique da Gabon. Kasashe hudu da suka kada kuri’ar kin amincewa da kudirin sun hada da Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Japan. Yayin da sauran kasashe 6 suka kauracewa kada kuri’ar.

Zaunannen wakilin kasar Rasha a MDD Vassily Nebenzia ya ce, tawagarsa ta yi matukar bakin ciki da sakamakon kada kuri’ar.(Ibrahim)