logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da a kara ba da taimako ga kasar Libya

2023-10-17 10:40:35 CMG Hausa

Wani wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su kara ba da taimako ga kasar Libya.

A baya-bayan nan dai bangarori daban-daban na kasar Libya sun yi kokarin inganta tattaunawa ta siyasa, da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, da kuma martani ga batun ambaliyar ruwa. Duk da haka, har yanzu suna fuskantar manyan kalubale. Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya da kwamitin sulhu na MDD su ba da karin goyon baya don taimakawa kasar Libya wajen shawo kan matsalolin. Ya bayyana muhimmancin ci gaba da gudanar da tattaunawa ta siyasa ga kwamitin sulhu.

Bangarori daban-daban a kasar Libya sun fara tattaunawa kan samar da taswirar zabe kuma majalisar wakilai, ko majalisar dokoki, sun amince da dokokin zaben.

Dai ya kara da cewa, kasarsa na fatan dukkan bangarorin za su karfafa sakamakon shawararin, da kawar da bambance-bambance, da ciyar da harkokin siyasa gaba, da samar da yanayin gudanar da zabe. (Yahaya)