logo

HAUSA

Yadda shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta taimaka wajen gudanar da gasar cin kofin Afirka

2023-10-17 20:52:53 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Za a fara gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin Afirka a kasar Cote d’Ivoire, daga ranar 13 ga watan Janairun badi. Na san abokanmu ‘yan Afirka da dama na sha’awar wasan kwallon kafa, wadanda ke Alla-Alla su isa filin gasar don kallon yadda za ta wakana.

Zanenmu na yau, ya nuna mana yadda filin wasa na San Pedro dake kasar Cote d’Ivoire, wanda ke cikin muhimman filayen wasa da za a gudanar da gasar. A watan da ya gabata ne, kamfanonin kasar Sin suka kammala gina filin wasan, tare da mika shi hannun kasar ta Cote d’Ivoire, kuma a kashegari, aka gudanar da daya daga cikin gasannin neman shiga gasar cin kofin Afirka a filin.

Filin wasa na San Pedro, na da fadin muraba’in mita dubu 24, wanda ke iya karbar masu kallo kimanin dubu 20. Ban da filin wasan, kamfanonin kasar Sin sun kuma gina filin horas da ‘yan wasa, da kauyen ‘yan wasa, don samar da wurin kwana da na horaswa ga ‘yan wasan da za su halarci gasar. Filin ba kawai ya kyautata karfin kasar Cote d’Ivoire wajen gudanar da manyan gasanni irin su Afirca Cup ba ne, har ma zai sa kaimi ga bunkasuwar ababen more rayuwa da suka shafi wasannin motsa jiki, da ma kyautata rayuwar al’umma.

Hadewa da juna da ababen more rayuwa, da ma karfafa fahimtar juna, na daga cikin muhimman fannoni na aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. Kasancewarsa wani muhimmin shirin hadin gwiwa a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, filin wasa na San Pedro ba kawai filin wasa ne na zamani ba, ya ma kasance misali da ke shaida yadda aka taimakawa al’ummar kasar Cote d’Ivoire wajen cimma burinsu ta fannin gudanar da wasanni, da kuma karfafa fahimtar juna a tsakanin jama’ar kasar Sin da ta kasashen Afirka, ta hanyar gina manyan ababen more rayuwa. (Mai Zane:Mustapha Bulama)