logo

HAUSA

Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Zama Nagge Dadi Goma

2023-10-17 20:01:29 CMG Hausa

Daga Abdulrazaq Yahuza

Kafin fara hadin gwiwa a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” a tsakanin Kasar Sin da Afirka, kimanin shekara 10 da suka gabata, galibin mutanen Afirka kan kwana su tashi da burin ganin yaushe za su more rayuwarsu irin yadda ‘yan kasashen da suka ci gaba a duniya suke yi.

Idan muka ga ko muka ji labarin kyawawan hanyoyi, tsaftataccen ruwan sha, sufuri mai inganci da sauran ababen more rayuwa a kasashen duniya, abin da ke fitowa daga bakinmu shi ne “wata miyar sai a makota”.

Amma daga shekarar 2013, yayin da Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, tunaninmu ya fara sauyawa saboda irin ayyukan raya kasa da shawarar ta fara samarwa a kasashen Afirka.

Egypt, na daga kasashen da suka fara rattaba hannu a shawarar ziri daya da hanya daya a 2013 kuma tuni take cin gajiyar lamarin. Akwai gagarumin aikin gina Sabon Babban Birnin Mulki da kuma yankin masana'antu na Suez Canal da zai yi kafada da kafada da takwarorinsa na duniya. Idan aka kammala gina sabon babban birnin zai rage cunkoso a Cairo, babban birnin kasar na yanzu. Kana yankin masana'antun zai kunshi tashoshin jiragen ruwa shida da masana'antu da cibiyoyin kasuwanci daban-daban da kuma gidajen jama'a.

Ita kuwa Nijeriya wacce ta shiga hadin gwiwar shawarar a 2018 kuma har ila yau a bana take cika shekaru 52 da kulla huldar difilomasiyya da kasar Sin, daga cikin ayyukan more rayuwar da ta ci gajiyarsu, akwai shahararren layin dogon nan da aka shimfida a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, da na Babban Birnin Tarayya Abuja, da na Legas zuwa Ibadan. Sai sabbin gine-ginen gudanarwa da tarbar fasinjoji da aka samar a manyan filayen jiragen sama na Kano, Abuja, Legas da Fatakwal. Kana ga tashar teku mai zurfi ta Lekki baya ga wasu ayyukan titunan mota da dama.

Wadannan ayyukan ci gaba sun kawo sauye-sauye masu ma'ana ga rayuwar 'Yan Nijeriya da dama. Misali, ma'aikatan da ba su da karfin zama a Abuja sun samu saukin zuwa aiki daga Kaduna zuwa Abuja, inda suke zuwa su dawo cikin yini guda.

Haka nan tashar Lekki da ta zama tashar teku mai zurfi mafi girma a Afirka ta Yamma, ana sa rai ta samar da kudin shiga Dala Biliyan 360 da ayyukan yi akalla 170,000.

Bugu da kari, sufurin jiragen kasa da aka kaddamar na cikin Birnin Legas ya taimaka wajen rage cunkoson da ake fama da shi a birnin daga lokacin da aka kaddamar zuwa yanzu, da rage gurbacewar iska a birnin da sauran harkoki na biyan bukatun yau da kullum na 'yan kasa.

Ba wannan ne ba kadai, akwai sauran ayyuka da dama da Kamfanonin Sin suka gudanar ko suke kan aiwatarwa da ke bayar da gudunmawa ga raya al'umma da tattalin arzikin kasa.

Ba a Nijeriya ne kawai, shawarar  “Ziri Daya da Hanya Daya” ke sauya rayuwar al'umma ba da tattalin arzikinsu.

A Kasar Uganda, gina babbar hanyar da ta tashi daga Kampala zuwa Entebbe wacce ta zama ta farko a kasar da ake samun kudin shiga da ita, da madatsun ruwa na samar da wutar lantarki a Karuma da Isimba da aikin fadada Filin Jiragen Sama na Entebbe sun saukaka sha'anin sufuri da bunkasa raya biranen kasar da kuma sada ta da sauran takwarorinta na Afirka, kana da ba da gudunmawa ga habakar tattalin arzikinta.

Haka zalika, a sakamakon “Ziri Daya da Hanya Daya”, 'yan kasar Senegal da ke fama da matsanancin karancin ruwan sha sun ci gajiyar rijiyoyi na zamani 251 da kasar Sin ta gina inda yanzu haka a kalla mutum miliyan biyu ke amfana, baya ga wasu 3,000 da suka samu aikin yi.

A Angola ma, sama da mutum 600,000 sun amfana da aikin jin kai na Kamfanin Layin Dogo na Kasar Sin (CRCC) wanda ya samar musu da ruwan sha na famfo, karon farko a rayuwarsu.

Tabbas, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta zama nagge dadi goma, bisa yadda kasashen duniya sama da 150 na yankin Turai, Asiya da Afirka suka amince tare da yin hadin gwiwa na ci gaba da Kasar Sin a karkashinta.