logo

HAUSA

Motsa jiki na tsawon minti 11 a ko wace rana na taimakawa rage hadarin mutuwar wuri (A)

2023-10-16 07:41:17 CMG Hausa

 

Wasu kan ce, ba su da lokacin motsa jiki. Yau madam Zhang Chuji, likita  da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta kawo mana labari mai dadi, muddin mutane suka dauki mintoci 11 kawai a ko wace rana suna motsa jiki bisa matsakaicin karfi, alal misali, yin tafiya cikin sauri, hawan keke, da yin rawa, to, zai taimaka wajen rage hadarin mutuwar wuri sakamakon ciwon zuciya, shan inna da ciwon kansa, da kaso 23.

Masu nazari daga sashen nazarin yaduwar cututtuka tsakanin al’umma da lafiya da dalilai da tsara manufofin dakilewa da kandagarkin cututtuka da inganta lafiyar al’umma karkashin shugabancin kwamitin nazarin ilmin likitanci na kasar Birtaniya, sun tattara bayanai daga rubutattun nazarce-nazarce 196 da aka kaddamar a fili, inda suka samu sakamakon da muka ambata a baya. Wadannan rubutattun nazarce-nazarce 196 sun shafi manyan nazarce-nazarce guda 94, wadanda suka shafi baligai fiye da miliyan 30 dangane da al’adarsu ta motsa jiki, yawan kamuwa da ciwo, yawan mutuwa da dai sauransu. Matsakaicin tsawon lokacin bibbiyarsu ya kai shekaru 10.

Masu nazarin sun yi lissafi sun gano cewa, idan baligai sun dauki mintoci a kalla 150 suna motsa jiki bisa matsakaicin karfi a ko wane mako, to, hadarin mutuwar wuri da suke da shi zai ragu da kaso 31. Ko da sun dauki mintoci 75 kawai a ko wane mako suna motsa jiki, kwatankwacin mintoci 11 a ko wace rana, to, zai rage hadarin mutuwar wuri da kaso 23, kana hadarin kamuwa da cututtukan da suka shafi jijiyoyin zuciya zai ragu da kaso 17, hadarin kamuwa da ciwon kansa zai ragu da kaso 7.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, idan ana daukar mintoci 11 ana motsa jiki a ko wace rana, to, za a rage hadarin kamuwa da ciwon kansa a ka da wuya, a bargo, a Cardia na ciki, da ciwon kansa na leukaemia da kaso 14 zuwa 26. Haka kuma, za a rage hadarin kamuwa da ciwon kansa a huhu, hanta, mahaifa, uwar hanji da mama da kaso 3 zuwa 11. (Tasallah Yuan)