logo

HAUSA

Masar ta yi tayin karbar taron bangarori da dama kan batun Falasdinu

2023-10-16 11:35:07 CMG Hausa

Fadar shugaban kasar Masar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kasar ta yi tayin karbar bakuncin wani taro na bangarori daban-daban, a wani mataki na magance halin da ake ciki na baya-bayan nan da kuma makomar batun Falasdinu.

Sanarwar ta kara da cewa, babu wata hanyar warware rikicin Palasdinu, illa kafa kasashe biyu, tana mai jaddada cewa, kasar Masar ta yi fatali da korar al’ummar Gaza da ake yi ko kuma kokarin aiwatar da kashe-kashen kan Palasdinawa inda ake cutar da kasashe makwabta.

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya ci gargadin cewa, mataki da Isra’ila ke dauka a zirin Gaza, ya zarce kare kai, inda ya rikide zuwa hukuncin ramuwar gamayya.

Shi ma shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya yi gargadin fadadar yakin, idan har Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza. Raisi ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Falasdinawa a 'yan kwanakin da suka gabata, ya kuma soki gwamnatin Faransa da hana jama’a gudanar da wani gangamin nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu a kasar.

A cikin wata sanarwa da majalisar kolin al’ummar Aljeriya ta fitar, ta bayyana cewa, kakakin majalisar Salah Goudjil, ya gana da wani babban jami'in kungiyar Hamas a jiya Lahadi, inda ya jaddada goyon bayan kasarsa ga al'ummar Palasdinu.

A nasa bangare, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a gaggauta kai agajin jin kai zuwa Gaza ba tare da nuna tsangwama ba, kana a saki mutanen da Hamas ke garkuwa da su.(Ibrahim)