logo

HAUSA

Shawarar BRI ta kawo manyan sauye-sauye a duniya cikin shekaru 10 da suka gabata

2023-10-16 13:51:11 CMG Hausa

 

Za a gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, wato BRF a takaice karo na 3 daga ranar 17 zuwa ranar 18 ga watan Oktoba. Alkaluman da Sin ta fitar a hukumance na nuna cewa, dandalin tattautawar na wannan karo ya jawo hankulan wakilan da suka fito daga kasashe fiye da 140 da kuma kungiyoyin duniya fiye da 30, su halarci taron don inganta ci gaba tare. Dalilin da ya sa dandalin tattaunawar ya shahara a duniya, a cikin shekaru 10 da suka gabata, aikin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, ya kawo sabbin sauye-sauye a duniya.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, an gudanar da ayyukan hadin gwiwa fiye da 3000 don gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, wato BRI a takaice, wadanda suka kai ga zuba jarin triliyoyin dalar Amurka. Ya zuwa karshen watan Yunin wannan shekara, Sin ta sanya hannu kan takardun hadin gwiwa fiye da 200 kan shirin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da kasashe fiye da 150 da kuma kungiyoyi fiye da 30.

Binciken bankin duniya ya nuna cewa, gudanar da shawarar “ziri daya da hanya daya” yadda ya kamata, zai kara habaka cinikayya tsakanin kasashen da suka amince da shawarar zuwa 4.1%, kana nan shekarar 2030, ana sa ran, shawarar za ta samarwa duniya kudaden shiga har dalar Amurka tiriliyan 1.6 a duk shekara. Kuma ana sa ran za ta cire mutane miliyan 7.6 daga kasashe masu hadin gwiwa daga matsanancin talauci.

Abubuwan da shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kawo ba moriyar tattalin arziki kawai ba ne, har ma da sabon tsarin mulki. Sin ta zuba jari don kafa asusun hanyar siliki, tare da kafa bankin zuba jari na kayayyakin more rayuwa na Asiya tare da kasashen da abin ya shafa, wanda ya fadada hanyoyin zuba jari da samar da kudade don gina kasashe tare da inganta tsarin tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya. Manufar shawarar “ziri daya da hanya daya” ita ce zamanintar da juna tare, tare da taimakawa wajen kara karfin kasashe na raya kansu. Daga raba kwarewar ci gaba zuwa horar da kwararru tare, daga bunkasa cinikayyar yanar gizo tsakanin kasa da kasa zuwa tattauna shirin ci gaba, Sin ta kawo sabbin damammaki ga duniya, tare da habaka hanyar zuwa zamanintarwa ta bil’adama.

Duk da cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta samo asali ne daga kasar Sin, amma shawara ce ta duniya baki daya, kuma ta kawo alheri ga dukkanin bil’adama. Kamar yadda kakakin majalisar al’ummar Serbia Vladimir Orlić ya ce, shawarar “ziri daya da hanya daya” hanya ce ta nan gaba. (Safiyah Ma)