logo

HAUSA

He Xiaoling: kwararriya mai gyaran layin dogo na karkashin kasa na kasar Sin

2023-10-16 15:01:40 CMG Hausa


He Xiaoling, kwararriya mai gyaran hanyar jirgin kasa ce kuma ma’aikaciyar ceton gaggawa dake aiki da kamfanin gina tituna da layukan dogo na Shanghai (STEC). Ta ce ta samu karin kwarin gwiwa daga ci gaba cikin sauri da kasar ke samu a fannin sufurin jiragen kasa da cikar muradun jama’a da ma burinsu na samun kyakkyawar makoma.

He ta kware a fannin gyara kuma ita ce shugabar tawagar masu kula da hanyoyin karkashin kasa na kamfanin STEC. Ta ce babanta injiniya ne a wannan bangare, kuma ya shiga aikin ginin hanyar karkashin kasa ta Dapu, wadda ita ce hanya ta farko da ta ratsa kogi a kasar Sin a shekarun 1960. Sai da ta fara aikinta, sannan ta fahimci aikin da mahaifinta ya yi, lamarin da ya sa ta yin alfahari da shi.

Ginin hanyar Dapu, wani muhimmin ci gaba ne a tarihin hanyoyin Shanghai, saboda ya ba mutane damar tuka mota su ratsa kogin Huangpu a karon farko.

Tsawon layin dogo na karkashin kasa na Shanghai ya zarce kilomita 800, wanda shi ne mafi tsawo a wani birni a duniya. Adadin layukan dogo na karkashin kasa dake karkashin kulawar tawagar He da abokan aikinta, ya karu daga 2 zuwa 6, kwatankwacin rabin tsawon daukacin layukan dogo dake cikin birnin.

Cikin shekaru 30 da suka gabata, He da tawagarta sun kasance tamkar likitocin zuciya, inda suke cikin shirin ko ta kwana a ko da yaushe, domin nazarin boyayyun abubuwan dake barazana ga tsaron da tabbatar da layukan dogo na aiki yadda ya kamata.

Bayan kammala karatu a shekarar 1993 daga jami’ar nazarin kimiyya da fasaha ta Shanghai da a yanzu aka kira da jami’ar Shanghai, He ta fara aiki a matsayin karamar ma’aikaciya a kamfanin STEC.

A yayin shekaru biyu na farko da ta yi a kamfanin STEC, He na zaune ne a ofis tana gudanar da ayyukan binciken kimiyya. Daga bisani, ta nemi a sauya mata aiki zuwa sashen gine-gine, ta yadda za ta shiga aikin kula da hanyoyi, bisa mayar da hankali kan kare samun matsaloli. Ta gano cewa, abu ne mai matukar muhimmanci a inganta amfani da sakamakon binciken da aka yi a fannin gine-gine.

Tun daga wancan lokaci, He da abokan aikinta suka dukufa kan bibiya da aikin gyaran hanyoyin karkashin kasa akai-akai, da aiki daga tsakar dare har zuwa safiya, domin tabbatar da tsaron fasinjoji.

Da farko, mutane 3 ne kadai ke aiki tare da He. A wancan lokaci, su kan yi jigilar kayayyakin gini da hannu, ta yadda ba za su kawo tsaiko ga harkoki a tashoshi da layukan jiragen karkashin kasa ba. A wani lokaci, suna bukatar aiki a wuri mai dumi, har na tsawon fiye da sa’o’i 10.

A shekaru 90 na karnin da ya gabata, He ta koma Shenzhen dake lardin Guangdong na kudancin kasar Sin, domin taimakawa birnin ginin layin dogo na karkashin kasa. A sannan, ita ce kadai mace dake aiki a wajen ginin, kuma ba ta nuna tsoro a lokacin da take gudanar da aiki mai wahala ba, ko da a cikin rami ne, wanda ke da zurfin mitoci 10.

A shekarar 2005, aka ba He matsayin shugabar sashen kula da hanyar karkashin kasa da ceton gaggawa na kamfanin STEC. Shekara daya bayan nan, tawagar He ta fara aikin kula da layin dogo na karkashin kasa mai lamba 6 na Shanghai.

Yayin taron baje koli na Shanghai a shekarar 2010, He ta jagoranci abokan aikinta wajen yin aikin dare, domin tabbatar da gudanar harkokin layukan jiragen kasa yadda ya kamata.  

He ta ce, yana da matukar muhimmanci su samu gogewa sosai da daukar sabbin matakai domin ginin layukan jirgin kasashin kasa daban daban, da za su dace da yanayi na musamman.

Misali, yayin wani rangadi, He ta gano tulin kasa mai damshi a wata hanyar jirgi, nan da nan kuma ta dauki matakan hana aukuwar hadari.

Akwai misalai da dama dake nuna kwarewar He da yadda take aiki tukuru, wadanda suka taka rawa wajen kare aukuwar haddura.

He ta kan yi aiki kafada da kafada da abokan aikinta domin magance matsaloli bisa wasu fasahohi da suka samu nasara. Sun kuma kirkiro fasahohin da suka yi amfani da su a hanyoyin karkashin kasa da dama, har sun kai ga samun lambar yabo.

Akwai mutane sama da 200 a cikin tawagar He. Ta fuskanci kalubale wajen ganin sun aminta da ita a matsayin shugabarsu. Ta kai ga samun hakan ne ta hanyar nuna karfin da take da shi a zahiri da kaifin basira da kwarewa da sauran wasu nagartattun siffofi.

A sakamakon haka, He kan sadaukar da lokaci mai yawa da karfi, wajen neman karin dabaru da ilimi.

Haka kuma, bisa gogewar da ta samu cikin gomman shekaru, ta kan koyar da matasa dake cikin tawagarta, domin taimaka musu zama kwararru kuma kashin bayan aiki a kamfanin STEC.

Har ila yau, ta shuka tsirrai da kayan lambu da dama a sansaninsu na kai ceton gaggawa, sannan ta kan gayyaci wadanda ba su je gida domin hutun murnar bikin bazara ba, su yi murnar bikin a sansanin.

Ta kan yawaita yabawa abokan aikinta da mijinta da danta, bisa goyon bayan da suka ba ta wajen gudanar da aikinta. Fahimta da goyon bayan da suke ba ta, tamkar haske ne a cikin ramuka.

Kididdiga ta nuna cewa, He da abokan aikinta sun bada kulawa tare da gyara layukan jirgin karkashin kasa 21 a fadin kasar, wadanda tsawonsu a jimlace ya kai kilomita 1000. Baya ga hakan, sun kafa wasu sansanonin aikin ceto a birane 6 a shekarar 2020.

He da tawagarta sun samar da cikakken taimako a Zhengzhou dake lardin Henan na tsakiyar kasar Sin a shekarar 2021, bayan birnin ya yi fama da ruwan saman da ya kai ga lalata dukiya da jikkatar mutane, duk da cewa ya kamata ta tsaya a Shanghai domin shiryawa tunkarar mahaukaciyar guguwa.

Zuwa yanzu, He ta jagoranci tawagarta wajen gudanar da ayyukan ceto sama da 500 a birane 26. Haka kuma, ita da abokan aikinta sun gina wani tsarin tsaron lafiyarsu yayin da suke karkashin kasa, lamarin da ya samu yabo daga ma’aikata na bangaren.

He ta samu lambobin yabo da dama a matakin kasa da na lardi, cikinsu akwai na lambar yabo ta ma’aikata mafiya nagarta na Sin, da ta mata mafiya nagarta na Sin, da ma’aikaciya abun koyi a birnin Shanghai. An ba ta lambobin yabon ne domin yabawa gagarumin gudunmuwar da ta bayar a gomman shekarun da ta shafe ta na aiki, har ma da sadaukarwarta wajen tabbatar da amincin bangaren sufurin jiragen karkashin kasa a kasar baki daya.  

A yayin hirar, He ta ce ci gaban da tsarin sufurin jirgin karkashin kasa na birnin Shanghai ke samu, na bukatar masu kula da shi su inganta amfani da fasahohi na zamani wajen inganta ayyukan kula da na gyara.

Bisa kokarin da He da abokan aikinta suka yi, an samar da wani tsarin kula dake amfani da fasahohi da na’urori na zamani a Shanghai, domin sa ido kan yadda ayyuka ke gudana a hanyar jiragen kasa, saboda akwai karancin lokacin binciken gani da ido da dare.

Amfani da fasahohi da na’urorin zamani sun taimakawa tawagar wajen kara gano boyayyun matsaloli dake da hadari, musamman wajen daukar matakan kandagarki domin tabbatar da amincin tsarin sufurin jiragen karkashin kasa a birnin Shanghai.

A lokacin da take bayani game da aikinta da yadda ta ji a shekaru 30 da ta shafe tana aiki, He ta ce ta kulla dangantaka ta kut da kut da birnin, haka kuma ta matukar jin dadin kasancewarta a nan.(Kande Gao)