logo

HAUSA

Yusuf Tuggar: Najeriya ta yi imanin shawarar “ziri daya da hanya daya” za ta inganta ci gban kasashen Afirka

2023-10-16 10:28:04 CMG Hausa

Yayin da ake shirin gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan raya shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3, kwanan baya wakiliyarmu Amina Xu ta zanta da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar. 

Yayin zantawar, ministan ya ce gwamnatin Najeriya na mutunta dangantakarta da Sin. a cikin 'yan shekarun nan, kasashen biyu sun ci gaba da yin hadin gwiwa mai amfani, tare da samun sakamako mai inganci. Najeriya ta yi imani cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatar za ta inganta ci gaban kasashen Afirka, tana kuma fatan hada kai da kasar Sin wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga bil’adama.

Bugu da kari, Tuggar ya yi imanin cewa, ya kamata kasashen biyu su karfafa hadin gwiwar harkokin kasa da kasa, don tabbatar da gaban zaman lafiya da ci gaban duniya. 

Ga zantawa da Yusuf Tuggar da wakiliyarmu.

(Safiyah Ma)