logo

HAUSA

Layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Jakarta da Bandung na Indonesiya

2023-10-15 17:39:54 CMG HAUSA

 

Indonesiya, kasar tsibirai mafi girma a duniya, tana fuskantar rashin ci gaba a fannin manyan ababen more rayuwa, saboda yanayin kasa da take da shi, matakin da ya yi tarnaki ga bunkasuwar kasar.

A shekarar 2015, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake ziyarar kasar, shugabannin kasashen biyu sun rattaba hannu kan takardar hadin kai, ta gina jirgin kasa mai saurin tafiya tsakanin Jakarta da Bandung.

A ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2022 yayin taron koli na G20, wannan jirgin kasa ya iso idon duniya a karon farko. An zana hoton alamar dabbar komodo, shahararriyar dabba a kasar a jikin sa, wanda hakan ya sa aka yi masa lakabi da “Komodo mai launin ja”.

Layin dogon ya hada babban birnin kasar Jakarta, da birni na 4 mafi girma a kasar wato Bandung, wanda hakan ya amfani mutane da yawan su ya kai miliyan 40.

Wannan jirgi ya kasance irinsa na farko da Sin ta gina a ketare, ta amfani da tsari, da fasaha, da kimiyya, da na’urori, da tsarin samar da kayayyaki irin na kasar Sin.

A matsayin jirgin kasa mai saurin tafiya na farko a Indonesiya, har ma da kudu maso gabashin Asiya, ya samar da damammaki masu kyau ga bunkasuwa da wadatar kasar, kuma ya bayyana niyyar Sin, ta more zarafi da sauran sassan duniya, don samun bunkasuwa tare. (Amina Xu)