logo

HAUSA

Shugaban Rasha: Shawarar ziri daya da hanya daya ta ingiza moriyar juna

2023-10-15 16:07:48 CMG Hausa

A kwanan baya ne shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya zanta da wakilin CMG a birnin Moscow, inda ya bayyana cewa, shawarar gina ziri daya da hanya daya tare, ta dace da tunanin raya tattalin arzikin Turai, da Asiya, da Rasha ta gabatar sosai, kuma kasashen da suka shiga shawarar za su ci gajiya, tare da samun moriyar juna.

Shugaba Putin ya kara da cewa, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar ne shekaru goma da suka gabata, wato a daidai lokacin da ya dace, saboda muradin shawarar shi ne kasashe daban daban su yi kokari tare domin cimma burikansu. Don haka ya yi maraba da shawarar, kuma Rasha na fatan yin kwazo da himma tare da kasar Sin, wajen tabbatar da aiwatar da shawarar.

Ya ce hakika tunanin raya tattalin arzikin Turai da Asiya da Rasha ta gabatar, da shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar suna da buri iri daya. (Jamila)