MDD: Zaman dar dar a Arewacin Mali na iya kawo tsaiko ga ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya
2023-10-15 16:08:05 CMG Hausa
Sashen watsa labarai na ofishin babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwa, game da yanayin rashin tabbas, da karuwar ayyukan kungiyoyin masu dauke da makamai a arewacin Mali, lamarin da a cewar ofishin na iya yin tarnaki, ga burin da ake da shi na kwashe dakarun tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar.
Ofishin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, ya ce halin da ake ciki a yanzu, ya haifar da koma baya ga ayyukan soji, da tawagar ta MINUSMA ke dauka ta sama, domin ba da damar ficewar dakarun yadda ya kamata.
Kaza lika, MDD ta tabbatar da aniyarta ta kwashe dakarun na MINUSMA nan zuwa ranar 31 ga watan Disamba, kamar dai yadda kwamitin tsaron MDD ya tsara, bayan gabatar da bukatar hakan da gwamnatin Mali ta yi.
Har ila yau, ofishin ya ce abun takaici ne, ganin yadda tun daga ranar 24 ga watan Satumbar da ya shude, aka hana jerin gwanon motocin da za su bar birnin Gao, zuwa garuruwan Aguelhok, da Tessalit, da Kidal motsawa, domin tafiya kwaso kayayyakin aiki da dakarun MDD, da sauran kasashe masu tallafawa suka samar.
Hakan a cewar ofishin zai shafi burin da ake da shi na kammala ficewar tawagar ta MINUSMA a kan lokaci. Duba da cewa akwai yiwuwar sojojin su fice ba tare da kwashe kayayyakin aikin ba. A cewar ofishin, hakan na iya hana tawagogin MDD masu aikin wanzar da zaman lafiya gudanar da ayyuka yadda ya kamata, a wasu kasashen na daban, dake bukatar irin wadannan kayayyakin aiki. (Saminu Alhassan)