logo

HAUSA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Yana Inganta

2023-10-14 17:08:33 CMG Hausa

A 'yan kwanakin da suka gabata ne, jirgin kasan dakon kaya na farko tsakanin Sin da Turai, ya isa birnin Shanghai dauke da kayayyakin da za a baje a bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na shida. Shi dai wannan jirgi ya taso ne daga birnin Duisburg na kasar Jamus dauke da TEU 70 na kwantenoni, wadanda darajarsu ta kai sama da kudin Euro miliyan 16.

Wannan na nufin cewa, bikin CIIE karo na shida da aka dade ana jira yana kara karatowa, wanda hakan zai kara sanya sabbin kuzari ga bunkasuwar cinikin waje na kasar Sin.

Alkaluman hukuma da aka fitar jiya Jumma’a na nuna cewa, darajar kayayyakin shige da fice na kasar Sin a rubu'i uku na farkon shekara, ta kai kudin Sin RMB yuan tiriliyan 30.8, wanda saurin karuwarta ya kusan yi daidai da na makamancin lokaci na shekarar bara. Tun daga farkon wannan shekara, farfadowar tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma baya, kuma ci gaban kasuwancin duniya ya fuskanci matsi da dama. A cikin wannan yanayi, cinikayyar waje ta kasar Sin "mai inganci" ba ta zo cikin sauki ba.

A halin yanzu, "sabbin abubuwa guda uku" da motoci masu amfani da wutar lantarki, da batirin lithium da kuma na’urorin tattara hasken rana ke wakilta, sun zama sabbin alamun cinikin waje na kasar Sin.

A rubu'i uku na farkon shekarar bana, darajar sabbin kayayyakin uku da kasar Sin ta fitar, ta kai yuan biliyan 798.99, wanda ya karu da kashi 41.7 bisa 100 kan na shekarar bara, kuma yawansu da ke cikin jimillar kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa ketare, ya karu da kashi 1.3 cikin 100 kan na shekarar bara, har ya kai kashi 4.5 bisa 100. Hakan ya kara sanya sabon kuzari a cinikin waje na kasar Sin.

Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ci gaba da farfadowa da ma inganta, baya ga aiwatar da wasu tsare-tsare da matakai yadda ya kamata, ana saran shigowa da fitar da kayayyaki za su ci gaba da karfafa kyakkyawan yanayin da ake ciki, da ci gaba da sanya kwanciyar hankali a harkokin cinikayyar duniya. (Ibrahim)