Yadda Shawarar “Ziri daya da hanya daya” ke ba da gudummawar raya tattalin arzikin kasashen da abin ya shafa
2023-10-14 14:28:47 CMG Hausa
Masu kallonmu, barkanmu da war haka! A shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin hada kai wajen gina “Zirin tattalin arziki na hanyar siliki”, da “Hanyar siliki kan teku na karni na 21”. Ya zuwa karshen watan Yuni na shekarar 2023, kasashe sama da 150 da kungiyoyin kasashen duniya sama da 30 sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da 200, bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”.
Cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin da kasashen da abin ya shafa, sun zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, lamarin da ya taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin kasashen, yayin da hakan ke kara kyautata zaman rayuwar al’ummominsu.
Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake halartar shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta sa bangarorin biyu cimma moriyar juna. Manyan kasuwannin kasar Sin sun samar da damammaki da dama ga kasashen. A halin yanzu kuma, yawan hajojin da ake shigowa da su daga kasashen sun kai rabin adadin hajojin da kasar Sin ta shigo daga kasashen ketare. Haka kuma, hadin gwiwar da kasar Sin ta yi da kasashe masu halartar shawarar “Ziri daya da hanya daya” a fannin cinikayya, ta ba da taimako ga kasashen wajen raya harkokin masana’antu, da ayyukan samar da kayayyaki.
Kana, bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kamfanonin kasar Sin sun dukufa wajen raya ayyukan gina ababen more rayuwa a kasashen da abin ya shafa, wadanda suka hada da fannonin zirga-zirga, da gina gidaje, da samar da wutar lantarki da sauransu.
Cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin da kasashen da suka halarci shawarar “Ziri daya da hanya daya”, sun kulla yarjejeniyoyin da darajarsu ta kai dallar Amurka triliyan 2, kuma, ya zuwa yanzu, an kammala shirye-shiryen da darajarsu ta kai dallar Amurka triliyan 1 da biliyan dari 3, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen kyautata zaman rayuwar al’ummomin wadannan kasashe. (Maryam)