logo

HAUSA

Daga Yiwu Zuwa Madrid

2023-10-14 21:27:24 CMG Hausa

Ranar 26 ga watan Satumban shekarar 2014 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Mariano Rajoy Brey, tsohon firaministan kasar Spain, inda a cewarsa, kasar Sin ta gayyaci Spain da ta shiga ayyukan ginawa da kuma tafiyar da layin dogo tsakanin birnin Yiwu na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin zuwa birnin Madrid na Spain, a kokarin daga matsayin hadin gwiwar kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

Kwanaki 53 ke nan bayan ganawar shugabannin 2, jirgin kasa na farko ya tashi daga birnin na Yiwu. Karo na farko da layin dogo ya hada Yiwu da ke nahiyar Asiya da Madrid da ke nahiyar Turai. An rage tsawon lokacin da ake dauka wajen yin jigilar kaya ta teku daga kusan watanni 2 zuwa kwanaki 21 kawai.

A shekarar 2022, a karon farko jimillar darajar cinikayya tsakanin Sin da Spain ta zarce dalar Amurka biliyan 50. Ya zuwa yanzu, jiragen kasa na kasar Sin da kasashen Turai sun bude hanyoyi 86, inda suka isa birane sama da 200 a kasashe da yankuna 25 na Turai. (Tasallah Yuan)