logo

HAUSA

MDD: Yanayin jin kai a Gaza yana ci gaba da tabarbarewa

2023-10-13 11:48:01 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne jami’an jin kai na Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana cewa, halin da ake ciki na jin kai a zirin Gaza na ci gaba da tabarbarewa sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.

Fiye da mutane 338,000 ne suka rasa matsugunansu, wanda ya karu da kashi 30 tun daga ranar Laraba. Sama da mutane 218,000 da suka rasa matsugunansu sun nemi mafaka a makarantun dake karkashin hukumar ’yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) a cewar ofishin kula da harkokin MDD (OCHA).

Sama da rukunin gidaje 2,500 ne aka lalata ko kuma aka ruguza baki daya yayin da kusan gidaje 23,000 suka sami matsakaici ko kananan lalacewa, a cewar ofishin.

A kalla cibiyoyin ilimi 88 aka kaiwa hari, ciki har da makarantun hukumar ’yan gudun hijira 18, biyu daga cikinsu an yi amfani da su a matsayin mafaka na gaggawa ga ’yan gudun hijira. Hakan na nufin cewa a ranaku shida a jere sama da yara 600,000 ba su samu damar daukar karatu ba a wuri mafi tsaro a Gaza, a cewar ofishin. (Yahaya)