logo

HAUSA

SON ta kawo shawarar dauri ba tare da cin tara ba ga dilolin gurbatattun kaya

2023-10-13 13:35:05 CMG Hausa

Hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta tarayyar Najeriya SON ta ce, ta gabatar da gyara kan dokar zartar da hukuncin dauri ba tare da cin tara ba ga dillalai masu shigo da gurbatattun kayayyaki cikin kasar.

Darakta janaral na hukumar Faruok Salim ne ya bayyana hakan jiya Alhamis a birnin Legas lokacin da ya jagoranci lalata wasu kayayyaki marasa inganci da aka shigo da su kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kayayyakin da aka lalata sun hada da tayoyin mota da wayoyin wutan lantarki da jarkokin man mota da sauran kayayyakin yau da kullum wanda kudinsu ya haura biliyoyin Naira.

Shugaban hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta Najeriya ya ci gaba da cewa, sun kai dokar gaban ’yan majalissar dokokin kasa domin yi mata gyara kuma tuni suka amince, abun da ya rage kawai shi ne sanya hannun shugaban kasa domin ta zama doka, kuma akwai kyakkyawan fatan shugaban zai rattabawa dokar hannu nan ba da jimawa ba.

“Tayoyin da aka kama wasun su a fuska za ka gan su kamar sabbi saboda an wanke su an goga masu maiko, wasu kuma sabbi ne amma abun takaici masu shigo da kayan su kan hada tayoyin fiye da daya a cikin taya guda. Hakan kuma ya kan rage ingancin wayoyin dake jikin tayoyin wanda hakan ya sanya muka ga da cewa mu lalata su gaban daya. Dogaronmu dai a nan shi ne dukkannin wadannan kaya suna da matukar barazana ga al’umma.”  (Garba Abdullahi Bagwai)