logo

HAUSA

Sin da Saudiyya na hadin gwiwar gina sabon birnin “Red Sea” karkashin hadin gwiwar shawarar “Ziri daya da hanya daya”

2023-10-13 11:07:40 CMG Hausa

A watan Janairun shekarar 2016, bisa gayyatar da sarkin masarautar Saudiyya Salman bin Abdul Aziz Al Saud ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki Saudiyya. A yayin ziyararsa, shugabannin kasashen biyu sun cimma matsayi daya, wajen karfafa mu’amalar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”.

Sa’an nan, a watan Afrilu na shekarar ta 2016, wato bayan watanni 3 da ziyarar ta shugaba Xi, Saudiyya ta wallafa “Burin da ake fatan cimmawa zuwa shekarar 2030”. Wato gina sabon birnin “Red Sea”, wani sabon birni da Sin da Saudiyya ke ginawa cikin hadin gwiwa.

An fara ginin wannan birni ne bisa muhimmin shirin hadin gwiwar Sin da Saudiya a fannin kare muhalli, da rage yawan hayaki mai dumama yanayi, kuma za a samar da wutar lantarki a wannan birni ta hanyar amfani da makamashi mai tsabta. Kaza lika bayan kammalar aikin a shekarar 2030, mutane kimanin miliyan 1 za su rika zuwa yawon shakatawa cikin sa a ko wace shekara, lamarin da ya nuna cewa, wannan birni zai kasance muhimmin mataki na cimma burin kasar Saudiyya nan zuwa shekarar 2030, da kuma nasarar muhimmin shirin dake gudana tsakanin Sin da Saudiyya bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”.(Mai Fassarawa: Maryam Yang)