logo

HAUSA

Wanzar Da Zaman Lafiya Ne Babban Aikin Da Ya Dace A Sanya Gaba A Gabas Ta Tsakiya

2023-10-12 17:33:49 CMG Hausa

Alkaluman baya bayan nan da kafofin watsa labarai ke fitarwa na nuna cewa, tuni adadin mutane da suka rasu, sakamakon dauki-ba-dadin dake aukuwa tsakanin sojojin Isra’ila da mayakan kungiyar Hamas sun haura 2,200 tare da jikkata wasu 8,000, tun bayan barkewar fada a ranar Asabar.

Mafi yawan masu fashin baki dai na cewa, yakin na wannan karo bai zo da mamaki ba, duba da har yanzu ba a kai ga cimma managarcin tsarin warware rikicin Isra’ila da Falasdinawa yadda ya kamata ba.

Kasashe irin su Sin da masu ra’ayi irin nata, sun sha nanata bukatar kawo karshen wannan takaddama ta hanyar siyasa, wato hawan teburin shawara, da ingiza kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kansu, wadanda za su baiwa Isra’ilawa da Falasdinawa damar zama da juna lami lafiya, kuma cikin ’yanci. To amma sabanin hakan, wasu daga kasashen yamma, sun ki baiwa wadannan shawarwari goyon bayan da ya dace, ko da a matsayinsu na daidaikun kasashe kawayen Isra’ila, ko kuma a dandalin kasa da kasa kamar na MDD.

Shaidar dake tabbatar da hakan ita ce yadda a ranar Talata, shugaban Amurka Joe Biden ya ayyana mika taimakon kayayyakin aikin soji ga Isra’ila, da nufin tallafa mata wajen murkushe hare-haren da Hamas ke kaddamarwa kan yankunanta, ko da yake shugaban na Amurka ya ce bai dace wata kasa ta yi amfani da sabon fadan da ya barke da nufin cimma wani buri na kashin kai ba.

Idan mun yi nazari da kyau, za mu ga cewa, Amurka ba ta sauya daga matsayarta ta raba kafa ba, domin kuwa idan har ba ta da burin amfani da wannan yaki a matsayin wata dama ta cimma burin kashin kai kamar yadda shugaba Biden ya ambata, to bai kamata ta yi gaggawar aikewa Isra’ila da kayan yaki ba, maimakon haka, kamata ya yi ta shige gaba wajen tabbatar da an tsagaita wuta, da kai zuciya nesa, tare da jan hankalin sassan biyu ga bukatar komawa shawarwari.

Bugu da kari, ya kamata Amurka, da sauran kasashen yamma irin su Jamus da Faransa, wadanda suka fito fili wajen bayyana takaicinsu ga sake barkewar fada, su waiwayi baya, su san cewa “Zama lafiya ya fi zama dan sarki”, su kuma goyi bayan kafuwar kasashe biyu a matsayin mataki mafi dacewa, na kawo karshen takaddamar Isra’ila da Falasdina bisa adalci, idan kuwa suka ki rungumar wannan shawara, to ko shakka babu duniya za ta ci gaba da kallon su a matsayin masu “Fakewa da guzuma domin harbin karsana”. (Saminu Alhassan)