logo

HAUSA

An kaddamar da gwamnatin hadaka a Isra’ila yayin da fada ke kara kazanta tsakanin sojin kasar da dakarun Hamas

2023-10-12 10:19:03 CMG Hausa

Kasar Isra’ila ta kaddamar da gwamnatin hadin kai da majalissar lura da yaki, a wani mataki na sanya ido kan tashin hankalin da ya barke, bayan da dakarun Hamas sun kaiwa yankunan Isra’ila hare-haren ba zata a karshen makon jiya, inda kuma nan take Isra’ila ta ci gaba da kaddamar da hare-hare ta sama kan Falasdinawa a zirin Gaza.

Sabuwar majalissar lura da yakin ta Isra’ila dai na kunshe da tsohon ministan tsaron kasar, kuma jagoran jam’iyyar hadin kan kasa ko National Unity party Benny Gantz, da wakilan gwamnatin firaminstan kasar mai ci Benjamin Netanyahu. Yayin da kuma mambobin majalissar lura da yakin suka hada da ministan tsaron kasar Yoav Gallant.

An kafa majalissar lura da yaki ta Isra’ila ne a gabar da Isra’ilawa ke ci gaba da sukar Netanyahu da gwamnatin sa, bisa zargin gazawa wajen aiwatar da ingantaccen shiri, da hangen nesa, na kare harin da aka kaiwa kasar a ranar Asabar, da ma rade-radin da ke yawo cewa, nan ba da jimawa ba sojojin kasar za su kaddamar da hare-hare ta kasa kan zirin Gaza.

Dauki ba dadin dake wakana ya riga ya haifar da dumbin asarar rayuka daga sassan biyu, inda adadin wadanda suka mutu a bangaren Isra’ila ya kai mutum 1,200, da kuma mutum 1,100 a bangaren Gaza. (Saminu Alhassan)