logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Borno: yanzu babu wani yanki a jihar da yake hannun Boko Haram

2023-10-12 09:25:26 CMG Hausa

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya tabbatar da cewa, a halin yanzu babu wani yanki a jihar da yake karkashin ’yan kungiyar Boko Haram.

Ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa lokacin da ya ziyarci gidan gwamnatin jihar dake birnin Maiduguri, inda ya ce, yanzu dukkan al’umomin jihar Borno suna karkashin jagorancin gwamnati.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Gwamnan na jihar Borno ya ci gaba da cewa, a watanni 18 da suka gabata ’yan kungiyar Boko Haram su dubu 140 ne tare da iyalansu suka mika wuya ga gwamnati, inda ya yabawa dakarun tsaron Najeriya bisa sadaukar da kansu wajen kokarin samar da dauwamammen zaman lafiya a jihar ta Borno.

“Za mu yi kokarin kyautata aiki tare da ku wajen kawo karshen hare-haren ta’addanci a wanann yanki cikin ikon Allah. Za mu yi nasarar cin galabar ’yan Boko Haram ne kuma ta hanyoyi kamar haka, daya daga cikin su shi ne kara karfafa juriyar al’umma, muddin hakan ba ta samu ba zai yi wahala mu iya samun galaba a kan ’yan Boko Haram.”

Ya tabbatar da ci gaba da samun cikakken hadin kan gwamnatin jihar ga rundunar sojin Najeriya a aikin da take yi na yaki da ’yan ta’adda a yankin.

Da yake jawabi, babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya jaddada cewa dakarun rundunar tsaro na kasa za su ci gaba da amfani da matakan sulhu da kuma na amfani da karfi wajen yaki da ’yan ta’adda a yankin.

Ya ja hankalin ’yan ta’addan cewa, kwanakin su na rayuwa a kirge suke, lokaci kawai muke jira da za mu kawar da su daga doron kasa, a don haka domin amfanuwar kansu, muna ba su shawara cewa ko su mika wuya, ko kuma su fice daga kasar baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)