logo

HAUSA

Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Inganta Kare Hakkin Dan Adam Yayin Samun Bunkasuwa

2023-10-12 21:24:43 CMG Hausa

Zaunanniyar tawagar Sin dake MDD ta gudanar da wani taro kan hakkin ci gaba, tare da hukumar gudanarwar kungiyar kasashe 'yan ba-ruwanmu a hedkwatar MDD a jiya Laraba. Yayin taron, zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya gabatar da jawabi dake da alaka da jigon, inda ya yi kira da a sanya batun ci gaba a muhimmin bangaren ajandar kasa da kasa, inganta kare hakkin dan Adam yayin samun bunkasuwa, da gaggauta gudanar da ajandar ci gaba mai dorewa na shekarar 2030, a kokarin inganta ci gaban kasa da kasa da aikin hakkin dan Adam.

Zaunannun wakilai da mataimakan wakilai daga kasashe fiye da 80 a MDD da jami’an MDD sun halarci taron tare da gabatar da jawabai. Kasashen duniya sun yaba da hanyar da Sin take bi da kuma sakamakon da ta samu wajen raya hakkin dan Adam, sun yi imanin cewa, nasarorin da Sin ta samu a fannonin ci gaban tattalin arzikin da kawar da talauci da sauransu sun kasance “abubuwan al’ajabi a duniya”, wadanda suka zama darussa masu amfani da kuma abin koyi ga sauran kasashe masu tasowa don tabbatar da hakkinsu na samun bunkasuwa.(Safiyah Ma)