logo

HAUSA

Shugabannin kasashen duniya na cike da kyakkyawan fata game da taron kasa da kasa na hadin gwiwar raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya

2023-10-12 10:45:36 CMG Hausa

Kasar Sin ta shirya gudanar da taron kasa da kasa karo na 3, na hadin gwiwar raya shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, a ranaikun 17 da 18 ga watan Oktoban nan a birnin Beijing fadar mulkin kasar.

Taken taron na wannan karo shi ne "Ingantaccen tsarin hadin gwiwa don gina shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da hada karfi wajen samun bunkasuwa da wadata". Ya zuwa yanzu, wakilai daga sama da kasashe 130, da sama da hukumomin kasa da kasa 30 sun bayyana aniyar su ta halartar taron.

Da yake tsokaci game da taron dake tafe, shugaban Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso, ya ce zai jagoranci babbar tawaga zuwa taron. A cewar sa shirin gina shawarar Ziri Daya da Hanya Daya zai haifar da babbar gajiya ga al’ummar Congo. Shugaba Sassou-Nguesso ya kara da cewa, Sin ta gina ababen more rayuwa masu tarin yawa a Congo, kuma kammalar wadannan ayyuka ya yi matukar inganta rayuwar al’ummar kasar sa.

Daga nan sai shugaban na Congo ya bayyana babbar hanyar mota mai lamba 1 da kasar Sin ta gina a kasar sa, a matsayin muhimmin aiki da ya hade birnin Brazzaville fadar mulkin kasar da birni na biyu mafi girma a kasar wato Pointe-Noire, da kuma yankin tsaunukan Mayombe. Wannan aiki a cewar sa zai taimakawa Congo wajen zama kasa mai karfi, mai wadata, kuma kasar da dukkanin ’ya’yan ta ke da ayyukan yi.

A nasaba bangare kuwa, ministan kudin kasar Habasha Ahmad Shide, yabawa hadin gwiwar Sin da Habasha ya yi, da ma ci gaban da aka samu cikin shekaru 10 da suka gabata, karkashin shawarar "Ziri daya da Hanya daya", yana mai fatan samun karin damammakin hadin gwiwar Habasha da Sin bayan taron karo na 3 dake tafe.  (Saminu Alhassan)