logo

HAUSA

Adadin mutanen da suka rasu sakamakon dauki ba dadi tsakanin sojojin Isra'ila da dakarun Falasdinawa na ta karuwa

2023-10-11 11:22:00 CMG Hausa

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ce ya zuwa jiya Talata, adadin Falasdinawan da aka hallaka sakamakon dauki ba dadin da ake yi tsakanin sojojin Isra'ila da dakarun Hamas a zirin Gaza, ya karu zuwa mutum 830, yayin da kuma aka jikkata mutum 4,250.

A bangaren Isra'ila kuwa, tashar talabijin ta kasar Kan TV, ta ce fadan ya haifar da kisan 'yan kasar a kalla 1,008, tun bayan da dakarun kungiyar Hamas suka fara kaddamar da hare haren ba zata a ranar Asabar.

Yayin da fadan ke kara kazanta, rundunar sojin Isra'ila ta ce a daren jiya Talata, jirgin saman Amurka na farko dauke da albarusai ya isa Isra'ila, a wani yunkuri na tallafawa kasar a yakin da take yi da dakarun Hamas masu iko a Gaza, da ma dakarun sa kai na Lebanon.  (Saminu Alhassan)