logo

HAUSA

Kasar Amurka ta sanar da dakatar da taimakonta na dalar Amurka miliyan 442 ga kasar Nijar

2023-10-11 10:52:48 CMG Hausa

 

Gwamnatin kasar Amurka ta dauki niyyar soke taimakonta na dalar Amurka miliyan 442 ga kasar Nijar, fiye da watanni biyu bayan juyin mulki. Sanarwar da ta fito a ranar jiya Talata 10 ga watan Oktoban shekarar 2023. Mataki dai ya zo a daidai lokacin da sabbin hukumomin Nijar suke fuskantar takunkumin kungiyar CEDEAO.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Sai dai wannan mataki bai shafi batun kwashe sojojin Amurka ba. Amma duk da haka, ta wannan dama kuma, kasar Amurka ta sanar a hukumance da amincewa da karbar mulkin kwamitin ceton kasa na CNSP ta hanyar juyin mulki, da ya faru a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, wanda ya kifar da tsohon shugaban kasar Mohamed Bazoum. Ganin cewa gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa wannan juyin mulkin ya sabawa tsarin mulkin dimokuradiya, shi ne dalilin daukar wannan mataki na dakatar da tallafin kudi da take baiwa jamhuriyar Nijar.

Kasar Amurka na daya daga cikin kasashen da suka bayyana damuwarsu kan matakin da shugabannin gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika CEDEAO ko ECOWAS suka dauka wajen amfani da karfin soja domin maido shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed kan mukaminsa. Sai dai wannan niyya ta kungiyar yammacin Afrika ba ta samu karbuwa ba daga yawancin al’umomin kasashen ECOWAS, ganin cewa mataki zai iyar janyo tashin hankali mai tsanani da zai iya bazuwa a yankin Sahel baki daya, dalilin ke nan da gwamnatin Amurka ta fi ba da fifiko kan sulhunta rikicin siyasar Nijar cikin ruwan sanyi.

Wannan matakin da Amurka ta dauka kan Nijar, ya biyo bayan takunkumin kungiyar CEDEAO da na kungiyar UEMOA suka dauka washe garin juyin mulkin.

Har yanzu gwamnatin Nijar ba ta ce uhum ba kan wannan mataki na Amurka na dakatar da tallafin kudin da take baiwa Nijar.

Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.