logo

HAUSA

Adadin Wadanda Suka Mutu A Falasdinu Sakamakon Hare-haren Isra'ila Ya Kai 1,078

2023-10-11 20:39:40 CMG Hausa

 

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa dake Ramallah ta sanar da cewa, adadin Palasdinawan da suka mutu da ma jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan, ya kai 1,078 da 5,314 bi da bi.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta bayyana cewa, daga cikin mutane 1,078 da suka mutu, 1055 sun kasance a zirin Gaza, tana mai cewa, wadanda suka jikkata a zirin Gaza sun kai 5,184.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Isra’ila ya bayyana Larabar nan cewa, a halin da ake ciki, adadin wadanda suka mutu a harin da kungiyar Hamas ta kai kan Isra'ila ya kai kimanin dubu 1 da 200. (Ibrahim).