logo

HAUSA

An zabi mambobin hukumar kare hakkin bil adama ta MDD

2023-10-11 10:49:33 CMG Hausa

An zabi kasashe 15 domin zama mambobin hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, yayin zaman taron MDDr na jiya Talata. Kasashen za su shafe wa’adin shekaru 3 tun daga 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa, a matsayin mambobin majalissar mai wakilai 47.

An gudanar da zaben mambobin ne ta hanyar kuri’un sirri, kuma kasashen Afirka da aka zaba su ne Burundi, da Kwadebuwa, da Ghana, da Malawi. Akwai kuma Sin, da Indonesia, da Japan, da Kuwait. Sai kuma Albania, da Bulgaria, da Brazil, da Cuba, da Dominican Republic. Akwai kuma Faransa, da Netherlands.

A wannan karo ma an sake zabar kasashen Sin, da Kwadebuwa, da Cuba, da Faransa, da Malawi, domin ci gaba da kasancewa mambobin wannan hukuma. Kaza lika, akwai kasashe 10 da za su kammala wakilci a hukumar a karshen shekarar nan. Kasashen su ne Gabon, da Senegal daga Afirka. Sai Nepal, da Pakistan, da Uzebekistan daga yankin Asiya da Pacific. Akwai kuma Czech Republic, da Ukraine daga gabashin Turai. Bolivia, da Mexico daga Latin Amurka da Caribbean. Sai kuma Birtaniya daga yammacin Turai da sauran kasashe.

Ana rarraba kujerun wakilcin hukumar kare hakkin bil adama ta MDD ne tsakanin yankunan duniya daban daban. Inda nahiyar Afirka da yankin Asiya da Pacific ke da mambobi 13. Sai Latin Amurka da Caribbean mai mambobi 8. Yayin da ake baiwa yankin yammacin Turai da sauran kasashe kujeru 7. Sai kuma gabashin Turai mai mambobi 6. (Saminu Alhassan)