logo

HAUSA

Charles Onunaiju: Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Sanya Sabon Ci Gaba A Najeriya

2023-10-11 20:21:38 CMG Hausa

Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya Charles Onunaiju, ya bayyana a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar, ta sanya sabon ci gaba a Najeriya, kasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, ta kuma samarwa kasar karin damammakin shiga harkokin tattalin arziki na duniya.

Onunaiju ya yi imanin cewa, kara shiga a dama da ita wajen raya shawarar cikin hadin gwiwa, zai sa Najeriya ta samu karin damammaki na samun darajar kasa da kasa, da kara aza harsashin bunkasa masana'antu. Yana mai cewa, inganta gina ababen more rayuwa a karkashin shawarar, sannu a hankali zai taimaka wa Najeriya canza fifikon da take da shi a fannin albarkatu da yawan jama'a zuwa ga ci gaban masana'antu.(Ibrahim)