logo

HAUSA

Ana fatan bangarorin Isra’ila da Falesdinu su kwantar da hankali su gaggauta kawo karshen tashin hankali

2023-10-11 09:27:18 CMG Hausa

Yanzu haka dai hankalin duniya ya karkarta ga kazamin fadan da ya barke tsakanin Isra’ila da Falasdinu, inda bayanai ke cewa an tabka hasarar rayuka tsakanin bangarorin biyu.

A nasu bangare kasar Sin da sauran kasashe masu kaunar zaman lafiya, sun damu matuka kan yadda zaman dar-dar da tashe-tashen hankula ke ci gaba da karuwa a tsakanin Falasdinu da Isra'ila, inda suka yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su kwantar da hankulansu, su kuma yi taka-tsantsan, tare da gaggauta kawo karshen tashin hankalin, don kare fararen hula, da kaucewa karuwar tabarbarewar halin da ake ciki.

Barkewar rikicin ya sake nuna cewa, lafawar zaman lafiya da aka samu, ba zai dore ba. Kuma, hanya mafi dacewa ta fita daga rikicin ta ta'allaka ne wajen aiwatar da shawarwarin kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu.

Kwamitin tsaron MDD ya gudanar da zaman gaggawa na sirri, bayan da dakarun Falasdinawa suka kaddamar da muggan hare-hare kan yankunan Isra’ila dake zirin Gaza. Cikin tsokacin da ya yi game da hakan, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga sassan da rikicin ya shafa da su kai zuciya nesa, tare da kaucewa rura wutar rikicin.

Shi ma babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kawo karshen yawan tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya, a dai-dai lokacin da rikicin Isra’ila da Falasdinu ya haddasa kisan sama da mutum 1600.

Ya ce rikicin sassan biyu na wannan karo yana da tushe, duba da cewa wutarsa ta ruru ne sannu a hankali, sakamakon tsawon lokaci da sassan biyu suka shafe suna sa-in-sa, kana an shafe shekaru 56 ana mamayar yankuna, ba tare da samar da wani sahihin tsari na siyasa domin warware takaddamar ba. Don haka ya zama wajibi Isra’ila ta cimma burinta na wanzar da tsaro bisa doka, yayin da a daya hannun ya zama tilas su ma al’ummar Falasdinawa su tabbatar da ganin tsari na gaskiya na kafuwar kasarsu.

Sanin kowa ne cewa, shawarwarin zaman lafiya na hakika ne kadai zai kai ga iya cimma halastattun burikan sassan biyu, kuma karkashin manufofin samar da tsaron sassan biyu, da burin kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kai, daidai da kudurorin MDD, da dokokin kasa da kasa, da yarjejeniyoyin da aka amince a baya ne za a iya wanzar da daidaito mai dorewa a wannan yanki, da ma sauran sassan gabas ta tsakiya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)