Sakamako da aka samu bayan gina shawarar ziri daya da hanya daya
2023-10-11 12:57:49 CMG Hausa
Kwanan baya tashar yanar gizo ta jaridar “Times” ta kasar Agentina, ta wallafa wani bayani mai taken “Cika shekaru goma da gina shawarar ziri daya da hanya daya: Damammakin kasashe masu tasowa da masu samun saurin bunkasuwa”, wanda a ciki aka yi bayani kan taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 3, wanda za a gudanar a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.
Kawo yanzu kasashe sama da 130, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30 sun riga sun tabbatar da aniyar su ta halartar taron.
Shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar gina zirin tattalin arziki kan hanyar siliki, da hanyar siliki ta kan teku a karni na 21, kuma ya zuwa karshen watan Yunin bana, gaba daya kasashe sama da 150, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30 sun daddale takardun hadin gwiwa sama da 200, bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kana adadin cinikayyar shige da fice dake tsakanin kasar Sin da wadannan kasashen sun zarta dalar Amurka triliyan 19.1. Ana iya cewa, kasashe da kungiyoyin da suka shiga shawarar suna kara karuwa a cikin shekaru goma da suka gabata.
Alal hakika, tun da farko kasashen da suka shiga shawarar sun fi mai da hankali ne ga kyautata zaman rayuwar al’ummun kasa da kasa. Kaza lika bankin duniya ya yi hasashen cewa, nan da shekarar 2030, kudaden da aka zuba bisa shawarar za su kubutar da mutane miliyan 7.6 daga kangin talauci mai tsanani, kuma za su fitar da mutane miliyan 32 daga kangin matsakaicin talauci, kana abu mafi muhimmanci shi ne, shawarar ta kara karfafa fahimtar juna dake tsakanin al’ummun kasashen, tare kuma da habaka cudanyar wayewar kai yadda ya kamata. (Jamila)