logo

HAUSA

Wasu gwamnonin jihohin Najeriya za su samar da rundunar tsaron musamman domin yaki da ’yan ta’adda

2023-10-11 10:31:59 CMG Hausa

 Gwamnnonin jihohin dake arewa maso yammacin Najeriya sun amince da murya guda wajen kafa rundunar tsaron musamman da za ta taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da ayyukan ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da satar shanu a jihohin su.

Gwamnonin sun amince da hakan ne yayin wani taro da suka gudanar jiya Talata a jihar Katsina tare kuma da sheda bikin kaddamar da irin wannan rundunar reshen jihar ta Katsina.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnoni 6 da suka fito daga shiyyar arewa maso yammacin Najeriya da kuma gwamnan jihar Yobe Mai-mala Buni wanda ya fito daga shiyyar arewa maso gabas suna daga cikin manyan bakin da suka sheda bikin, wanda kuma ya sami wakilcin jami’ai daga hukumomin tsaro na jiha da na tarayya.

Dukkan gwamnonin dai sun yarda da samar da doka da za ta ba su damar kafa wannan runduna, ta amfani da majalissun dokokinsu.

Da yake jawabi, gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda ya ce, dakarun tsaron musamman su 1,456 da aka kaddamar za su tallafawa sauran ma’aikatan tsaro na gwamnatin tarayya da suke aiki a jihar wajen dakile karuwar ayyukan ta’addanci.

Ya ce, dakarun na musamman sun samu horo ne daga sojoji, da jami’an tsaro na DSS a kan dabarun binciken sirri tare da kai farmaki ga maboyar irin wadannan bata-gari.

“Muna godiya ga Allah da ya ba mu dama a yau muka kaddamar da wadannan matasa kamar yadda muka yi alkawari lokacin da muka zagaye kananan hukumomi 34 a jihar Katsina. Mun yi wa mutanen jihar Katsina alkawarin cewa idan duk za mu kashe kudin jihar Katsina mu kawo tsaro a jihar Katsina. In Allah ya yarda za mu kashe kuma Allah zai taimaka mana. Yau rana ta zo da muka fara yaye rukuni na farko na wadannan jami’ai namu na kanmu wadanda suka yarda, iyayensu suka yarda, danginsu suka yarda, matansu suka yarda su zo su kare mutane da dukiyoyinsu a jihar Katsina.”

Gwamna Dr Dikko Radda ya yaba bisa hadin kan da majalissar dokokin jihar ta ba shi wajen hanzartar samar da dokar da ta ba shi damar kirkirar rundunar tsaron ta musamman. (Garba Abdulahi Bagwai)