logo

HAUSA

Wanda ya shuka zamba, shi zai yi girbinta

2023-10-11 20:50:33 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

 Tun bayan da Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya na tashar Fukushima cikin teku, kasar ta fuskanci matsala wajen sayar da abincin ruwanta. Bisa labaran da kafofin yada labarai na kasar suka bayar, an ce, a wasu ma’adanai na wasu kamfanonin sarrafa abincin ruwa na kasar, tarin abincin ruwa na Scallop da dai sauransu sun kusan kai rufin ma’adanan da ke da tsayin mita 8.

An ce, a shekarar bara, gaba dayan kudin abincin ruwa da Japan ta sayar ga kasashen duniya ya kai dala biliyan 1.97. Amma tun bayan da Japan din ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, yawan abincin ruwan da kasar ke sayarwa ga waje ya ragu da matukar yawa, har ma wasu masanan sun yi hasashen raguwar za ta iya kai kaso 50%. Ban da wannan, sakamakon yadda sassan kasa da kasa ke nuna kyamar matakin na Japan, harkokin yawon shakatawa na kasar ma na fuskantar munanan asarori.

Sinawa kan ce “an tsinci ridi, a yayin da kuma aka yi watsi da kankana”, wajen bayyana yadda akan sha babbar hasara sakamakon neman cin karamar riba, to, abin da Japan ke yi ke nan yanzu, sakamakon yadda ta zubar da dagwalon nukiliyarta cikin teku don neman yin tsimin kudi, amma a sa’i daya, tana kashe makudan kudade wajen wanke kanta daga zarge-zarge da ake mata, tare kuma da shan munanan hasarori ta fannonin tattalin arziki. Lallai ma iya cewa, wanda ya shuka zamba, shi zai yi girbinta.

Tun daga ranar 5 ga wata, a zagaye na biyu ne Japan ta sake fara zubar da ruwan dagwalon nukiliyarta cikin teku, aikin da za ta shafe kimanin kwanaki 17 tana yi a wannan zagaye. Gaba dayan ruwan dagwalon nukiliya da ake ajiye da shi a tashar Fukushima ya kai sama da ton miliyan 1.3, kuma an yi hasashen za a shafe a kalla shekaru 30 kafin an zubar da gaba dayansa cikin teku. Don haka, da wuya mu iya hasashen yadda tekunan duniyarmu za su kasance, kuma ko halittun teku za su ci gaba da rayuwa ko a’a, da kuma yaya duniyarmu za ta kasance, da ma wace masifa matakin zai janyo wa dan Adam.

Muna yi wa gwamnatin Japan gargadi da ta dakatar da wannan mugun aikin nan da nan, kuma ta dauki matakan da suka dace, don kiyaye teku na dukkanin ’yan Adam. (Mai Zane:Mustapha Bulama)