logo

HAUSA

Babban jami’in Afirka ta kudu: Shawarar ziri daya da hanya daya na zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka

2023-10-10 15:12:55 CMG Hausa

Kwanan baya mataimakin shugaban majalisar dokokin al’ummar kasar Afirka ta kudu Solomon Lechesa Tsenoli ya yi tsokacin cewa, shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar ta habaka cudanya tsakanin kasashen Afirka, kuma ta kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar Afirka, don haka tana da ma’ana matuka ga ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu.

Tsenoli ya ba da misli da layin dogo da ya hada Mombasa da Nairobi dake kasar Kenya cewa, manyan kayayyakin more rayuwar al’umma da aka gina bisa tsarin shawarar ziri daya da hanya daya sun taka rawar gani ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma a kasashen Afirka, a sa’i daya kuma, shawarar ta ba da gudummowa wajen kyautata dangantakar dake tsakanin kasa da kasa.

Jami’in ya kara da cewa, kasashen Afirka da kasar Sin suna da buri iri daya, a sanadin haka hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu yana kara habaka yadda ya kamata. Yana sa ran hadin gwiwar dake tsakaninsu zai kara zurfafa, ta yadda za a ingiza ci gaban nahiyar Afirka, gami da duk duniya baki daya. (Jamila)