logo

HAUSA

CMG Za Ta Nunawa Duniya Yadda Ake Hadin Gwiwar Moriyar Juna

2023-10-10 17:54:05 CMG Hausa

Gabanin babban taron kasa da kasa dangane da hadin gwiwa bisa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya dake cika shekaru 10 a bana, babban rukunin gidajen talabijin da rediyo na kasar Sin CMG, ya kaddamar da hadin gwiwa da kafofin watsa labarai na kasashen dake aiwatar da shawarar.

Hakika waka a bakin mai ita ta fi dadi. Wannan hadin gwiwa zai bada damar bayar da cikakku kuma sahihan labaran kasar Sin da ainihin yanayin da ake ciki dangane da shawarar kamar yadda ya kamata, ga al’ummomin duniya. Haka kuma, zai taka rawa wajen wayar da kan kasashen duniya game da irin alfanun shawarar da ayyukan da ake aiwatarwa a karkashinta.

A ganina, kasar Sin ba ta samu yabon da ya kamata game da ayyuka da tallafi da shawarwari da ma dabarun samar da ci gaba da zaman lafiya da take gabatarwa a duniya, saboda yadda wasu kasashe suka dukufa wajen shafa mata bakin fenti. A yanzu, kasar Sin da ta jagoranci gabatar da shawarar tare da raya ta, za ta samu damar bayar da labari da bakinta ta hannun CMG, yayin da kafofin watsa labarai na kasashen da shawarar ta shafa, za su watsa wadannan sahihan labarai da bayanai ga al’ummominsu, lamarin da zai sa jama’ar kasa da kasa su kyautata fahimtarsu kan kasar Sin.

Kasancewar kafofin yada labarai, matsayin masu ilmantarwa da wayar da kan al’umma, wannan hadin gwiwa zai taimaka gaya wajen kore jita-jita da dukkan wasu labarai na karya da ake yadawa. Ta hakan ne kuma, al’ummomin duniya za su gane matsayin kasar Sin na mai neman daidaito da moriyar juna tsakanin kasa da kasa dake da burin gina al’umma mai makoma ta bai daya.

Da yake gabatar da jawabi, shugaban CMG Shen Haixiong, ya ce CMG ta sa hannu kan yarjejeniyoyin watsa labaru da kafofin yada labaru 682 daga kasashe 15 domin yada shirye-shirye gane da shawarar. Wannan gagarumin ci gaba ne la’akari da cewa, cikar shawarar shekaru goma ta nuna cewa tana kara bunkasa, don haka akwai bukatar kara wayar da kai game da burika da manufofin kasar Sin na hadin gwiwa, domin al’ummun duniya su gane cewa, yanzu an shiga wani babi na hadin gwiwar moriyar juna bisa adalci da daidaito, maimakon wanda aka saba gani na cin nasara daga faduwar wani bangare.

Ko shakka babu, ina da yakinin bisa irin jajircewarta, CMG za ta cimma burinta, kuma duniya za ta fahimci ainihin kasar Sin.