logo

HAUSA

Sojojin Faransa sun fara janyewa daga jamhuriyar Nijar

2023-10-10 20:01:31 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, kasar Faransa ta fara janye sojojinta daga jamhuriyar Nijar, bayan da shugabannin juyin mulkin kasar dake yammacin Afirka da suka yi juyin mulki a watan Yuli, suka ba su umarnin ficewa daga kasar.

Mai magana da yawun babban hafsan hafsoshin kasar Faransa ya ce, ayarin farko na dakarun sun fice, yayin da yake tabbatar da sanarwar da rundunar sojin Nijar din ta fitar jiya Litinin, wadda a cikinta ta ce, dakarun kasar Faransa 1,400 za su fara ficewa daga yau Talata, karkashin rakiyar sojojin jamhuriyar Nijar. (Ibrahim)