Iran da Sudan su amince su dawo da huldar diflomasiyya bayan shafe shekaru bakwai suna rashin jituwa
2023-10-10 10:01:16 CMG Hausa
A jiya Litinin ne kasashen Iran da Sudan suka sanar da maido da huldar diflomasiyyarsu, shekaru bakwai bayan yankewar huldar.
Jamhuriyar Sudan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun yanke shawarar maido da huldar diflomasiyya a tsakaninsu domin cimma maradun kasashen biyu biyo bayan wasu muhimman tuntuba da suka yi a cikin watannin da suka gabata, a cewar wani sanarwar da ma’aikatun harkokin wajen kasashen biyu suka fitar tare a ranar Litinin.
Sudan ta katse huldar diflomasiyya da Iran a shekarar 2016 bayan matakin da Saudiyya ta dauka na yanke hulda da Tehran a wannan shekarar.
A watan Janairun 2016 ne Saudiyya ta yanke huldar diflomasiyya da Iran bayan harin da aka kaiwa ofishin jakadancin kasar a Tehran, bayan da masarautar ta zartar da hukuncin kisa kan wani malamin Shi'a. (Yahaya)