logo

HAUSA

Kamfanin CGC na kasar Sin zai gudanar da aikin ruwa da zai samar da lita dubu 480 na ruwa a kullum a birnin Abuja

2023-10-09 10:51:18 CMG Hausa

Kamfanin gine-gine da ayyukan samar da ruwan sha na kasar Sin CGC ya ce, zai gudanar da aikin shimfida karin bututun ruwa da zai taimaka wajen samar da karin ruwa har lita dubu 480 a rana ga unguwannin dake cikin birnin Abuja.

Kamfanin wanda yake da hedikwata a birnin Abuja ya tabbatar da hakan ne ranar Asabar ta makon jiya cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafin intanet na kungiyar tarayyar Afrika tare kuma da raba ta ga wasu kafofin watsa labarai a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kamar dai yadda yake kunshe cikin sanarwa, kamfanin na China Geo-Construction ya ce, ya dade yana gudanar da aiyukan da suke da tasirin gaske wajen kyautata rayuwar ’yan Najeriya, inda ya tabbatar da cewa, a shekarar 2001 ya gina sama da matatun ruwa guda 100 a jihohin kasar 36 wanda kuma hakan ya bayar da damar bunkasa sha’anin ruwan sha ga mutane har miliyan 70.

Kamfanin na CGC ya kara da cewa muhimmancin aikin ya wuce na batun samar da ruwa kawai a birnin Abuja, zai kara inganta tsarin rayuwar al’umma a birnin tare kuma da kyautata harkokin kiwon lafiya.

Haka kuma aikin zai samar da aikin yi na kai tsaye ga sama da ’yan kasa guda dubu guda.

Kamfanin ya bayyana cewa a watan Mayun 2021 gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da babbar tashar samar da ruwa ta birnin Abuja wanda kamfanin ya gina karkashin tallafin bankin lura da harkokin shigowa da fitar da kayyayaki na kasar Sin da kuma hukumar lura da babban birnin tarayyar Abuja. Daga wannan tashar samar da ruwan ne kamfanin zai samar da karin bututun ruwa wanda zai kara adadin ruwan da ake samu yanzu haka a birnin na Abuja.

Tuni dai mazauna birnin na Abuja suka fara bayyana ra’ayoyinsu game da wannan aiki.

 “Malam Halliru dake nan babban birnin tarayyar Abuja. Karancin ruwa da muke fama da shi, shi ne ya kawo masu kasuwanci wato ’yan ga ruwa suke debowa a rijiyoyin burtsatsai ko kuma su je famfo suna debo shi jarga-jarga masu launin ruwan dorawa kowanne jarga daya suna sayarwa a kan naira dari biyu-biyu.”

“Abdullahi Musa. Gaskiya muna fuskantar matsalar ruwa sosai ana bangaren gwagwala, saboda akwai unguwanni da yawa da za ka same su ga ruwan amma ba a samu mai kyau sai yawanci na rijiyoyi in kuma borehole ne kuma za ka samu mutane da yawa a wajen suna layi.” (Garba Abdullahi Bagwai)