logo

HAUSA

Gasar wasannin Asiya ta Hangzhou kyauta ce ta musamman da kasar Sin ta bai wa duniya

2023-10-09 16:49:52 CMG Hausa

A daren yau Lahadi 8 ga wata ne, aka shirya bikin rufe gasar wasannin motsa jiki ta Asiya karo na 19 a birnin Hangzhou, hedkwatar lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin.

A cikin kwanaki 16 da suka gabata, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka, tare da gabatar wa duniya wata gagarumar gasar mai "halayen Sin, da salon Asiya, da kuma ban sha’awa". Har ila yau, duniya ma ta samu kyakkyawar fahimta, game da kasar Sin ta hanyar wannan gasa mafi girma da aka yi a Asiya.