logo

HAUSA

Tinkarar Kalubalen Duniya Ta Hanyar Haɗin Gwiwar Aikin Gona Na Shawarar Ziri Ɗaya Da Hanya Ɗaya

2023-10-09 22:48:24 CMG Hausa

Tun daga shekarar 2013, ƙasar Sin ta hanyar shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” ko BRI a taƙaice, wanda shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar, da nufin ƙarfafa ababen more rayuwa, da cinikayya da zuba jari, ta ƙulla haɗin gwiwa a fannin aikin noma tare da ƙasashe da dama da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa daban-daban, kawo yanzu, ta ƙulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a fannin aikin noma da ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sama da 90, kuma ta gudanar da ayyukan zuba jari a aikin noma sama da 650 a ƙasashen abokan hulɗar BRI da darajar ta kai dalar Amurka biliyan 14.  

Tun lokacin da aka gabatar da shawarar, wato haɗin gwiwar aikin gona na BRI, ya ƙarfafa ayyukan ƙasa da ƙasa da ma na duniya da aka jinginawa kawar da shingayen ci gaba a fannin aikin gona da samar da ababen more rayuwa gami da ingantacciyar hanyar sufuri don jigilar amfanin gona zuwa kasuwanni, da inganta haɗin gwiwar bincike a fannin kimiyyar aikin gona da inganta rumbunan ajiyar hatsi da ban ruwa da sauransu, tare da gabatar wa manoma yadda ake gudanar da ayyukan noma na zamani da kayan fasaha waɗanda ke sauƙaƙa aikin noma da haɓaka aikin noma mai ɗorewa. 

Bugu da ƙari, a cikin shekaru 10 da suka gabata, ƙasar Sin ta tura kwararrun masana aikin gona sama da 2,000 zuwa ƙasashe sama da 70, tare da koyar da su fasahohin noman shinkafa, da na leman kwaɗo da dai sauransu. A cikin wannan lokacin, an horar da manoma sama da 100,000 kuma sama da miliyan 1 sun samu tallafin kai tsaye don magance matsalolin da manoma da ma'aikata daban-daban suke fuskanta a tsarin darajar abinci. A sa'i daya kuma, a dukkan matakai guda hudu na tsarin tabbatar da wadatar abinci wanda ya kunshi ayyukan samar da kayayyakin amfanin gona, da suka hada da samar da iri da shuka, da sarrafa su, da kuma isar da amfanin gona ga abokan cinikayya, ƙoƙarin da ƙasar Sin ta jagoranta ya tinkari ƙalubalen da aka shafe shekaru da dama ake fama da su, waɗanda suka kawo cikas ga bunkasuwar fannin aikin gona da masana'antu masu alaƙa.

A yawancin ƙasashe masu ƙananan ƙarfi da masu matsakaitan kuɗin shiga, inda akasarin ma'aikata suka tsunduma cikin aikin noma wanda ya kasance sama da kashi 25 cikin 100 na GDPn su, haɗin gwiwar aikin gona na BRI mai nasaba da musayar fasahohin noma da zuba jarin noma, da zuba jari a ayyukan samar da ababen more rayuwa da kuma hanzarta daidaita manufofin siyasa, yana baiwa wadannan ƙasashe masu tasowa, waɗanda ke fama da kalubalen tsarin, wata dama ta musamman na samun ci gaba mai ɗorewa ta hanyar noma, da shiga sabbin kasuwanni da manyan kasuwanni, da ƙarfafa samar da ayyukan yi, da inganta samar da abinci.

Hakazalika, haɗin gwiwar aikin gona na BRI, musamman ga ƙasashen da ke yankuna masu fama da talauci ya zama rigakafin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga samar da abinci da kawar da fatara. Duk da cewa a halin yanzu, haɗin gwiwar aikin gona na BRI na da jerin nasarorin da aka samu a duk fadin ƙasashen Afirka da Asiya, ƙoƙarin da ƙasar Sin ke jagoranta zai iya ƙara inganta samar da abinci a duniya, da kawar da matsanancin talauci ta hanyar faɗaɗa haɗin gwiwar da sauran ƙasashen duniya.   

A watan Oktoban nan ne ake sa ran taron haɗin gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa karo na uku na shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” zai haɗa ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma bikin cika shekaru 10 da kafa ƙungiyar BRI. Taron zai zama wata muhimmiyar hanya ga masu tsara manufofi, abokan raya ƙasa, da sauran masu ruwa da tsaki, don yin musayar kwarewa, da buɗe sabbin damammaki na samun bunƙasuwa a ƙarƙashin ƙoƙarin da ƙasar Sin ke jagoranta na tinkarar ƙalubalen duniya. (Muhammed Yahaya)