Wakilin Sin ya yi kira ga dukkanin sassa da su kai zuciya nesa a rikicin Falasdinu da Isra’ila
2023-10-09 11:13:09 CMG Hausa
A jiya Lahadi ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da zaman gaggawa na sirri, bayan da dakarun Falasdinawa suka kaddamar da muggan hare hare kan yankunan Isra’ila dake zirin Gaza.
Cikin tsokacin da ya yi game da hakan, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga sassan da rikicin ya shafa da su kai zuciya nesa, tare da kaucewa rura wutar rikicin.
Zhang ya kara da cewa, Sin ta yi matukar damuwa bisa dauki ba dadin da ya barke tsakanin sojojin Isra’ila da dakarun Falasdinu a Gaza, wanda hakan ya sabbaba rasuwar fararen hula masu yawa. Ya ce Sin ta damu da yiwuwar kara kazantar fadan.
Daga nan sai jami’in ya jaddada kira ga dukkanin sassan da rikicin ya shafa, da su dakile ta’azzarar fadan, su kuma amincewa matakan tsagaita bude wuta. Kaza lika su rungumi matakan ingiza kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kai ba tare da wani bata lokaci ba.
Da yammacin jiya Lahadi, kafofin watsa labaran Isra’ila da dama sun bayyana cewa, sabon fada ya kara rincabewa tsakanin sassan biyu, wanda hakan ya haifar da kisan al’ummar Isra’ila sama da 700.
A daya bangaren kuma, hukumar kiwon lafiya ta Falasdinawa dake zirin Gaza, ta fitar da sanarwa a daren jiyan, wadda a ciki ta bayyana cewa, harin sojojin Isra’ila a zirin na Gaza, ya hallaka a kalla mutane 413 tare da jikkata wasu 2300. (Saminu Alhassan)