logo

HAUSA

Jami’ i: Sojojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga 31 a cikin mako daya

2023-10-09 10:16:53 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne wani jami’i ya sanar da cewa, sojojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga 31 a farmaki da suka kai a lokuta daban-daban a yankin arewacin kasar a makon da ya gabata.

A wata sanarwar da kakakin rundunar Edward Buba ya fitar, ya ce sojojin sun kuma kama wasu 81.

Buba ya kara da cewa, sojojin sun kubutar da a kalla mutane 10 da kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram dake yankin arewa maso gabashin Najeriya ke garkuwa da su.

Jam’in ya kara da cewa, “Sojoji ta hanyar ayyukansu, suna ci gaba da samun galaba a kan ’yan tada kayar baya da ta’addanci da nufin tabbatar da tsaron kasa daga masu tada kayar baya domin samu ci gaban kasa.” (Muhammed Yahaya)