Sabon rikicin Falasdinu da Isra'ila ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 600
2023-10-08 20:51:51 CMG Hausa
Alkaluman kididdigar da ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Isra’ila ta fitar yau da safe na cewa, sabon rikicin da ya barke tsakanin Falasdinu da Isra'ila ya yi sanadiyar mutuwar fiye da 'yan Isra'ila 300, tare da jikkata sama da mutane 1,800, kana an yi garkuwa da ‘yan Isra'ila da dama a zirin Gaza. A wannan rana, ma’aikatar kiwon lafiya ta yankin Gaza ta Palesdinu ta bayar da sanarwar cewa, mutane 313 sun mutu a sakamakon harin da sojojin Isra’ila suka kai a zirin Gaza, tare da jikkata mutane 1990.
A cewar sanarwar da sojojin Isra’ila suka fitar a yau, an ci gaba da harba makaman roka daga zirin Gaza zuwa cikin Isra’ila a wannan rana, kuma an ci gaba da jin karar hare-hare ta sama a wurare da dama na Isra’ila.
Wani jami’in hukumar leken asiri ta sojojin kasar Lebanon ya tabbatar a yau cewa, an dakatar da musayar wuta a tsakanin mayakan Hezbollah na Lebanon da sojojin Isra’ila bayan shafe tsawon awa daya da rabi ana gwabzawa. Wannan jami’i ya ce, sojojin Isra’ila sun kai hari ta sama a wurare da dama dake kudu maso gabashin kasar Lebanon, sai babu wanda ya mutu ko ya ji rauni ya zuwa yanzu. (Zainab)