logo

HAUSA

Yawan mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar Afghanistan ya zarce 2400

2023-10-08 21:35:18 CMG Hausa

A ranar 8 ga wata bisa agogon wurin, Mullah Janan Shaeq, kakakin ma’aikatar kula da bala’u daga Indallahi ta gwamnatin rikon kwarya ta kasar Afghanistan ya tabbatar da cewa, mutane fiye da 2400 ne suka mutu, yayin da 2000 kuma suka jikkata, sakamakon wata girgizar kasa mai karfin gaske da ta afku a lardin Herat da ke yammacin kasar Afghanistan jiya Asabar.

A sa’i daya kuma, Janan Shaeq ya tabbatar da cewa, alkaluman fiye da mutane 9000 da a baya a bayyana a taron manema labarai cewa, sun ji raunuka ba daidai ba ne.

A cewar cibiyar bayar da bayanai kan girgizar kasa ta kasar Sin, girgizar kasa guda biyu masu karfin maki 6.2 ne suka afkawa kasar Afghanistan jiya Asabar 7 ga wata.(Kande Gao)