logo

HAUSA

Turai: rashin isasshen motsa jiki na haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 10 da bai kamata a ce sun mutu ba a ko wace shekara

2023-10-08 16:51:20 CGTN Hausa

 

Mutane masu dimbin yawa da ke zaune a kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai EU ba sa motsa jiki da yawa, lamarin da ke haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 10 da bai kamata a ce sun mutu ba a ko wace shekara.

Fiye da sulusin mutanen da suke zaune a kasashe mambobin kungiyar EU ba sa motsa jiki bisa matsakaicin karfi ko babban karfi cikin mintoci dari 1 da 50 a ko wane mako, abun da hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ta ba da shawarar a yi. Idan wadanda ba sa motsa jiki isasshe a Turai sun bi shawarar WHO, to da wasu fiye da dubu 10 sun tsira daga mutuwar wuri, har ma matsakaicin tsawon rayukan mutane a kasashe mambobin kungiyar EU zai tsawaita da watanni 2.

Motsa jiki kullum, yana daya daga cikin dalilai masu muhimmanci da suke sanyawa a kasance cikin koshin lafiya a jiki da ma tunani. Kana kuma motsa jiki kan kare mutane daga kamuwa da ciwon sukari, wasu cututtukan kansa na musamman da dai sauransu.

Idan mutane su kan dauki mintoci dari 1 da 50 suna motsa jiki a ko wane mako, to, ya zuwa shekarar 2050, mutane fiye da miliyan 3 da dubu 500 za su tsira daga kamuwa da ciwon bakin ciki, wasu fiye da miliyan 3 da dubu 800 kuma za su kaucewa kamuwa da cututtukan da suka shafi jijiyoyin zuciya.

Abin bakin ciki shi ne, yanzu mutane da yawansu ya kai kaso 40 kawai wadanda suke zama a kasashe mambobin kungiyar EU ne suke motsa jiki kullum, kuma akwai bambanci sosai tsakanin kasashe da kuma maza da mata. A kasar Finland, baligan da yawansu ya kai kashi 2 cikin kashi 3 suna motsa jiki kullum, yayin da a sauran kasashen, yawan wadanda su kan motsa jiki kullum ya kai kashi 1 cikin kashi 5 ne kawai. Har ila yau kuma yawan mazan da su kan motsa jiki kullum ya fi yawan matan da su kan motsa jiki, musamman ma tsakanin matasa. A cikin ‘yan shekaru 15 zuwa 24 da haihuwa, mazan da yawansu ya kai kaso 73 ne suke motsa jiki a kalla sau daya a ko wane mako, yayin da yawan matan da suke motsa jiki a kalla sau daya a ko wane mako ya kai kaso 58 kacal.

Haka zalika kudin shiga shi ma ya na tasiri kan ko ana motsa jiki kullum ko a’a. Mutane masu samun albashi da yawansu ya kai kaso 24 su kan motsa jiki kullum, yayin da masu samun kudin shiga da yawa da yawansu ya kai kaso 51 ne suke motsa jiki kullum. Lalle matalauta ba su da lokacin motsa jiki. (Tasallah Yuan)